Yadda budurwa mai shekara 15 ta mutu suna tsakar lalata da wani mutum a cikin mota


Wata budurwa mai shekara 15 da haihuwa ta mutu yayin da suke tsaka da yin lalata da wani mutum mai shekara 26 a cikin mota.

Duk da yake yansanda na jiran sakamakon rahotun Likita na Post-mortem kan musabbabin mutuwar budurwar. Sai dai mutane da dama na hasashen cewa watakila ta mutu ne sakamakon gazawar zuciya.

An garzaya zuwa asibiti da Gabrielly Dickson Alves Nascimento ranar Alhamis 29 ga watan Yuli, bayan wanda suke lalata tare ya lura cewa budurwar ta mutu.

Likitoci a asibitin UPA Jardim Casquiero da ke Cubatão, São Paulo, sun lura cewa budurwar ta yi fama  da cutar zuciya kuma ta sami gazawar zuciya nan take zuciyarta ya daina aiki. Ta mutu da sanyin safiyar ranar 30 ga watan Yuli.

Likitoci sun sami jini a al'aurarta lokacin nazarin jikinta a asibiti, sai dai babu alamar cewa an yi amfani da tashin hankali a jikinta.

Babu wata alamar cewa yansanda sun tuhumi wanda ke saduwa da ita kafin ta mutu. Domin a kasar Brazil ka'idadden shekara na saduwa da yardar juna shi ne shekara 14.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari