Type Here to Get Search Results !

Yadda bajimin sa ya hargitsa taron gasar Pareti na masu yi wa kasa hidima a jihar kudu (Bidiyo)


Wani Sa ya haddasa rudani a gasar Pareti da ya gudana a sansanin horar da masu yi wa kasa hidima NYSC orientation camp a jihar Ogun ranar Alhamis 11 ga watan Agusta. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Rahotanni sun ce komai yana tafiya daidai, haka kawai aka gan Sa ya shigo fili da gudu yana neman wanda zai fuskanta, yayin da masu yi wa kasa hidima da ke jerin layin Pareti suka watse suna ihu wasu na sheka dariya.

Daga bisani tare da taimakon sojin da ke sansanin, an kama Sa kuma komai ya koma daidai.

Kalli bidiyon lamarin a kasa 

 

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies