An tsinci gawar babban Limamin Atiba, a Ijebu Ode, Alhaji Musafau Bakare, bayan wasu yan bindiga sun sace shi. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.
Ana samun mabanbantan rahotanni kan yadda yan bindigan suka dauke Limamin cikin daren ranar Laraba 11 ga watan Agusta.
Yansanda sun gano gawarsa a cikin sabuwar mota da ya saya kirar Toyota Highlander da sanyin safiyar Alhamis a yankin Obalaende da ke Birnin Ijebu Ode.
An bizine Limamin da karfe 10 na safiyar ranar Alhamis.
Rubuta ra ayin ka