Wani Gwamna ya shiga dakin taron jam'iiyar PDP ba zato ba tsammani, duba abin da ya faru


Yayin da ake cikin taron dattijan jam'iyyar PDP domin lalubo hanyar warware rikicin da ya kunno kai, anga gwamnan Rivers Nyesom Wike, ya shiga ɗakin taron ba zato ba tsammani.

Vanguard ta ruwaito cewa mutane da dama sunga isar Wike sakateriyar yayin da ake rade-radin cewa yana cikin waɗanda suka matsa a tunbuke shugaban PDP na yanzu, Uche Secondus. Taron dai na mambobin kwamitin amintattu ne wato BoT kuma sun kira taron ne domin tattaunawa kan abubuwan dake faruwa a cikin jam'iyyar PDP. Shugaban PDP, Uche Secondus da Gwamna Wike na jihar Rivers

The nation ra tuwaito cewa shigar gwamna Wike ba tare da tsammani ba ya jawo rudani domin gwamnoni basu cikin mambobin BoT kuma basu halartar taron BoT.
 
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan Rivers ɗin ya tattaka zuwa ciki dakin taron kwamitin zartarwa (NEC) inda ake gudanar da taron a dai-dai lokacin da Secondus yake jawabin buɗewa.

Mahalarta taron sun koma kallon gwamnan wanda ya nemi wurin zama cikin mahalarta taron ya zauna. Sai dai har zuwa yanzun babu wani cikakken bayani kan cewa ko mambobin BoT ne suka gayyaci gwamnan.

Source: Legit

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN