Yan bindiga sun sace iyayen kakakin majalisar dokokin Jihar Zamfara, duba yadda ta faru


A labarinta da ta wallafa, shifin BBC Hausa ta ruwaito cewa yan bindiga sun sace iyayen kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mai magana da yawun majalisar dokokin Jihar ta Zamfara Mustapha Jafaru Ƙaura ne ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin.

"Da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Laraba ne 'yan bindiga suka shiga wasu ƙauyuka a garin magarya, amma daga baya suka dawo suka shiga gidan mahaifin kakakin majalisa Nasiru Mu'azu Magarya.

"Ba su kai ga iya shiga gidan ba kai tsaye sai da suka yi amfani da manyan makamai suka harbi wayar da aka zagaye gidan da ita sannan suka samu shiga," in ji Mustapha Ƙaura.

Ƙaura ya ce an sace mahaifin Kakagin majalisar wanda yake rike da matsayin magajin garin magarya tare da wasu mutane shida da ke zaman fada.

An tambayi Ƙaura dangane da rahotannin da ke cewa an tafi da mahaifiyar kakakin, sai ya ce "tabbas tana cikin mutane shida da na ce an dauka an tafi da su."

Amma dai ya ce babu ko daya daga cikin 'ya'yansa da aka tafi da su kamar yadda rahotanni ke bayyana wa.

Har yanzu dai 'yan bindigar ba su kira kowa ba, kuma babu wata hanya da za a yi tubtubarsu.

Ya zuwa yanzu Mustapha Jafaru ya ce yanayin garin Magarya ya sauya, kowa yana cikin jimami.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro a kasar.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari