Wani bala'i ya sake fada wa yan Boko Haram, fiye da 100 a cikinsu sun mutu a jamhuriyar Nijar,


Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce dakarun kasar sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram sama da dari daya a yankin kudu maso yammacin kasar. BBC Hausa ta ruwaito.

Wata sanarwa da rundunar sojin kasa ta kasar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata ta ce lamarin ya faru ne a yankin Torodi da ke kan iyaka da Burkina Faso.

Sanarwar ta ce sojojin kasar 19 sun mutu yayin harin.

Ta kara da cewa dakarun sojin sun kai harin ne domin mayar da martani kan kisan da mayakan Boko Haram suka yi wa sojojin kasar ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Kazalika sojojin, karkashin shirin "Billougol Boni", wato "hukunta Boni' sun lalata makamai da motoci da baburan 'yan kungiyar ta Boko Haram.

Da ma dai yankin na Yammacin Jamhuriyar Nijar ya dade yana fama da hare-haren 'yan ta'adda da ke da sansanoni a arewacin Mali tun 2017.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN