An sake kashe 'mutane da dama' a sabon rikicin da ya ɓarke a Jos


Hukumomi a jihar ta Filato da ke tsakiyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane da dama sakamakon harin da wasu "ɓata-gari" suka kai a kauyen Yelwan Zangam da ke karamar hukumar Jos Ta Arewa ranar Litinin da daddare. BBC Hausa ta ruwaito.

Kwamishin Watsa Labarai na jihar, Mr Dan Manjang, wanda ya shaida wa BBC Hausa wannan labarin, ya ce kawo yanzu ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu da wadanda suka jikkata ba.

Sai dai wasu kafafen watsa labaran Najeriya sun ce an kashe fiye da mutum 30 yayin harin.

Mr Manjang ya kara da cewa ɓata-garin "sun kona wadanda za su kona suka na kashewa. Akwai wata gada ma da aka yi ta da katako take hada kauyen zuwa wasu yankunan, sun lalata ta don kada su bari jami'an tsaro su ketara su je wannan kauyen."

A cewarsa, an kama mutum goma da ake zargi da kai harin kuma tuni aka soma gudanar da bincike.

Sai dai ya ce yanzu haka ana zaman zulumi a yankin, ko da yake hukumomi suna bai wa jama'a hakuri don kada su tayar da tarzoma.

Ya kara da cewa mataimakin gwamnan jihar da wasu manyan jami'an gwamnati, cikinsu har da shi kansa kwamishinan watsa labaran suna kan hanyar zuwa kauyen domin ganin hakikanin abin da ya faru.

Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako biyu bayan wasu matasa da ake zargi 'yan kabilar Iregwe ne sun kashe mutum 25 matafiya Musulmai da ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya daga Jihar Bauchi bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci wanda Sheikh Dahiru Bauchi yake gudanarwa.

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari