Tsawa ta kashe yara mata 2 Yan uwan juna a harabar makarantar Islamiyya


Tsawa ta kashe wasu Yara mata Yan uwan juna guda biyu a garin Ikirun da ke karamar hukumar Ifelodun a jihar Ogun. Shafin labarai na isyaku.com ya wallafa.

The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Unguwar Ogo-Oluwa na Orisa Elejin da karfe 4:30 na yammma ranar Lahadi 29 ga watan Agusta.

Shugaban karamar hukumar Ifelodun,  Hassan Okanlawon, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce bayani da ya samu bayan isarsa wajen da lamarin ya faru ya nuna cewa yaran suna zaune tare ka Kakarsu.

Ta aikesu su je su sayo kayan miya. Lokacin da suke ratsawa a cikin wani filin kwallo da ke harabar wata Makarantar Islamiyya, sai tsawa ta fada masu suka mutu nan take.

Ya ce masu bautar "Sango" allan tsawa sun dakatar da shi daga daukar gawar yaran daga wajen da lamarin ya faru.

Ya ce matsafan na kan hanyarsu ta zuwa wajen domin gudanar da addu'oi a wajen kafin a dauki gawar yaran.


Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari