Ina fatan mutuwar ɗana za ta kawo karshen matsalolin Najeriya - Sanata Na'Allah


Sanata Bala Ibn Na'Allah, ɗan majalisar dattawan Najeriya da ake zargi wasu da kashe babban ɗansa, Abdulkareem a gidansa da ke Malali a Kaduna, ya ce yana fatan mutuwar ɗan nasa ta kawo karshen matsalolin Najeriya. BBC Hausa ta wallafa.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ya ce ran ɗansa bai fi na kowanne ɗan Najeriya ba.

Ya ce: "Maharan sun kutsa gidan ɗana ta rufin kwano suka makure shi har ya mutu. Ni da iyalina ba za mu manta da wannan rashi ba kuma za mu ci gaba da masa addu'a, saboda mutumin kirki ne".

Sanata Na'Allah da ke wakiltr Kebbi ta Kudu shi ne shugaban kwamitin harkokin sojin sama a majalisar dattawa, kuma baya ƙasar lokacin da aka kashe ɗan nasa kuma wadanda suka kashe shi ba sa dauke da bindiga.

A jiya ne dai aka samu rahotan hallaka ɗan sanatan mai shekara 36 a gidansa da ke titin Umar Gwandu a Malali na jihar Kaduna.

Ƴan sanda sun ce maharan sun tsere da motarsa kirar Lexus SUV bayan hallaka shi.

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN