Hasashe na ci gaba da haska Osinbajo a matsayin magajin Buhari mafi cancanta


Yayin da ake tattaunawa game da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023, masana sun bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar da yafi nagarta, kamar yadda yazo a kuri'ar da jaridar ThisDay ta yi.

Kuri'ar ya biyo bayan hirar da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida yayi da gidan talabijin na Arise TV akan wanda zai zama shugaban Najeriya a 2023.

Osinbajo shi ya cancanci zama shugaban kasa

Baya ga cancantar ilimi, Babangida ya ambaci shekaru da gogewa a matsayin muhimman abubuwan da za su sa a zabi wanda zai maye gurbin Buhari a 2023, inda ya bayyana a sarari cewa ya kamata 'yan Najeriya su zabi mutum mai kuzari wanda bai haura shekaru 60 ba.

Kuri'ar da jaridar ta wallafa a ranar Litinin ta kawo wasu fitattun 'yan Najeriya, tare da Osinbajo cikinsu a matsayin wadanda suka cancanta su rike manyan mukamai a nan gaba.

Sauran wadanda aka kawo sun hada da Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwunmi Adesina da Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed.

Hakazalika da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, da gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, da sauransu.

Gina sharhin su kan sharuddan da tsohon shugaban na soji Babangida, su ne: tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, Dakta Sam Amadi, ya ce Osinbajo ya fi cancanta fiye da sauran dukkan mutane 30 da aka lissafa a cikin rahoton ThisDay.

Source: Legit News

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN