Shirin Ciyar Da Dalibai: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Tantance ‘Yan Firamare 339,642 A Kebbi


Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin tantance dalibai 339,642 na makarantun firamare a Jihar Kebbi don samun addadin kididdigar daliban da ta ke ciyar wa a makarantun Firamare na Jihar. Jaridar Leadership Hausa ta wallafa.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wakilin Ma’aikatar Jinkai da Kuma ba da agajin gaggawa ga wadanda Bala’i ya shafa a kasar Nijeriya a karkashin tsarin ciyar da daliban Firamare a duk fadin kasar nan, Aminu Attahiru Zagga yayin zantawarsa da manema Labarai a ziyararsa zuwa wasu makarantun Firamare a karamar hukumar Birnin Kebbi da karamar hukumar Kalgo don ganin yadda aikin tantancewr ke tafiya.

Aminu Zagga ya ce, “Wannan tsarin ciyar da daliban makarantun Firamare a duk fadin kasar Nijeriya an bullo dashi ne tun shekarar 2016 a karkashin jagoranci Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a yanza haka muna da kididdiga ta dalibai Miliyan 9 a duk fadin kasar nan, amma bisa ga umurnin Shugaban kasa zamu kara yawan masu amfana da shirin ciyarwa zuwa Miliyan 10, inji Aminu Attahiru Zagga yayin zantawa da manema labarai a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a wasu makarantun Firamare a Birnin Kebbi da Kalgo”.

Ya kara da cewa, “Makasudin bullowa da tsarin ciyar wa a makarantun Firamare don kara yawan yara a makarantun Firamare na gwamnatin a duk fadin jihohin kasarnan da kuma bunkasar kananan Masana’antu da manoma domin abincin da ake ciyar da daliban abincin gida ne da manoman kasar Nijeriya suka noma, inji shi”.

“Kazalika a Jihar Kebbi zamu tantance daliban Firamare 339,642 a duk fadin Jihar don samun kididdigar daliban da ake ciyarwa a jihar” inji shi.

Saboda hakan ya yi kira ga iyayen yara da su tabbatar da sun sanya yaransu a makarantun Firamare na gwamnatin wanda a kalla za a ciyar da kowane yaro sau daya a cikin sa’o’in da yake a makaranta. Ya kuma ja kunnan mata masu dafa abinci da su tabbatar da suna bai wa daliban tsaftataccen abinci mai gida jiki.

Ya samu rakiyar Darakta Hukumar wayar da kai wato NOA, Mista Joseph Yaro Machika da kuma wakili daga hukumar yi wa kasa hidima reshen Jihar. Makarantun Firamare da ya kai ziyarar sun hada da Atiku Bagudu Science Model Firamare, Linzamiyya model Firamare da ke cikin karamar hukumar Birnin Kebbi, sai kuma Kalgo model Firamare kan ganin irin yadda aikin tantance dalibai ke gudana.

daya daga cikin matan da ke dafa abinci a makarantar Linzamiyya model Firamare da ke cikin Birnin Kebbi, Zainab Bello Sarki ta ce” Ina dafa abincin daliban 61 a makarantar, amma yanzu muna bukatar a karawa masu dafa abinci kudi domin a lokacin da aka dauke mu aikin dafa abinci kayan abinci basu yi tsada ba, yanzu ko sun yi tsada, inji ta.

Daga nan ta ce muna godiya ga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin wannan tsarin da ya fito dashi ya samar da ayyukan yi ga mutane da yawa a jihohin kasar nan.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE