"Generation Z" Duba rukunin matasan da basa ganin kowa da gashi tsakanin matasan Najeriya


Za a iya cewa tarbiyya ta yi faɗuwar baƙar tasa a wannan zamanin da muke ciki a tsakanin al'ummarmu.

Mace da aka sani a matsayin wacce za ta zama uwa wata rana har ma ta yi tarbiyya, amma an zo gabar da a kan samu yanayi da har ta kai munzalin aure tata tarbiyyar ba ta gama tsayawa da kafafunta ba.

Ko a kwanaki a Aisha Falke mai shafin Northern Hibiscuss a Facebook da Instagram, ta ce ƙorafe-ƙorafen da ake kai mata kan ƙarancin tarbiyya sun yi yawa.

Ta ce masu korafin sun ce mafi yawan 'yan matan zamanin nan ba sa ganin kowa da gashi.

Ga dai bayanin da ta yi a shafin nata:

"Maganar gaskiya tarbiyya a arewa ta sukurkuce. Generation Z (waɗanda aka haifa daga shekarar 1995 zuwa 2010), ba sa gannin kowa da gashi (daga mazan har matan).

"Amma a yau zan yi magana ne a kan matan. Kun ga na farko ba sa shiga kicin, iyaye mata tarbiyyar da aka ba su sun niƙe sun ajiye a ƙarƙashin akwati sun bar yara sai abin da suka ga dama suke yi.

"Ba sa ganin girman kowa sai mama da baba. Kannen uwa da na uba da yayyensu kuwa ko oho. Ba a koya musu ba.

"Wani irin kallo suke yi wani shi ba harara ba ba kallo kai tsaye ba. Dama babu batun rusunawa a gaida babba. A tsaye suke ƙiƙam kamar sandar ba'are.

"A ganinsu ma bai zama dole su gaida kowa ba, gani suke kamar ana shiga rayuwarsu ne.

"Mace wai sai ta kai shekara 18 har a yi mata aure, amma indomie wannan mai aiki ce za ta dafa mata. Sai ta ce ta me aikin ta fi dadi. Wanki kuwa ba ta taɓa iron ba wai ƙona ta yake yi.

"Ko ɗan kamfanta da rigar mama mai aiki ce ke wanke Undies wannan se me aiki ta wanke. Gyaran ɗaki kuwa sai ta tashi wurin ƙarfe 3 na yamma sannan mai aiki za ta shiga a share a gyara gado.

"Kar a zo kuma batun lura da mai gida. Uwa ba ta jawo ƴarta a jiki ta ga yadda kike yi wa babanta. Hada abincin mai gida, yanda ake yi duk ba ta sani ba.

"To irin waɗannan ƴan matan ne za a ɗauka a kai gidan aure kuma a samu kyakkyawar zamantakewa?," kamar yadda Falke ta faɗa.

Aisha Falke ta ce cikin irin ƙorafe-ƙorafen da ta taɓa ji da suka shafi lalacewar tarbiyyar mata har da na wata sabuwar amarya da ta cewa surukarta: "ke ba uwata ba ce don haka ba ki da damar yi min yadda kike so."

Mu a zamaninmu ranar da kika gwada ɗaya daga cikin waɗannan matsalolin da Falke ta zayyano ai ranar za ki gane shayi ruwa ne.

Ina mafita?

Mace fa ita ce ginshikin gina gida da iyali. Kenan akwai bukatar komawa kan teburi domin sake zana taswirar inda muka sa gaba

Malama Juwairiyya, wata fitacciyar malamar Islama a Bauchin Najeriya ta ce, dole sai shugabannin al'umma da suka hada da sarakuna da alakalai da 'yan siyasa da malamai su tashi tsaye don gyara tarbiyyar matasa a zamanin nan.

Ta ce "ba zai yiwu a ce sarki ko malami da ake ganin shi jagora ne ba sannan a ce a gidansa ana ganin abubuwa na rashin tarbiyya da ya gagara magancewa ba.

"Ya kamata a ce daga gidajensu ake fara ganin tsari mai kyau na tarbiyya da ginuwarta," in ji malamar.

Sannna ta ja hankalin iyaye musamman mata da cewa su dinga kula da shige da ficen 'ya'yansu. Su kuma jajirce wajen ɗora su a kan hanya ta gari.

"Abin kunya a wannan zamanin za a ga uwa ita kanta ba ta kintsu ba ta wajen yanayin sutura da mu'amalarta, balle kuma ta gyara ƴaƴanta.

"Dole sai mu iyaye mata mun sake janyo 'ya'yanmu a jiki muna nuna musu hanyoyi masu kyau, da gwada musu yadda za su girmama na gaba da su, da yadda za su zauna da mutane lafiya," in ji Malama Juwairiyya.

To wai wace ma irin mace ce maza ke rububi?

Wani matashi da na tattauna da shi mai suna Usmaan ya ce a zamanin nan ya zama wajibi maza su sake yin nazari kan nazari kafin su auri yarinya.

"Ni a matsayina na namiji zan fi so na auri mace mai kunya da ladabi da ganin girman na gaba da ita, mai kawaici, mili ilimin addini da na boko kuma take amfani da su.

"Yanzu maɗigo ya yi yawa tsakanin al'umma dole mu kula da yanayin irin wacce za mu aura.

"Ba na son mace da ta cika rawar kai da kinibibi. Ba na son 'yar ina da biki ko suna, wacce duk taro sai an gan ta," in ji Usman.

Ra'ayinsa ya yi daidai da na dumbin samarin da na ji ta bakinsu.

Ya kamata iyaye mu tashi tsaye mu koya wa 'ya'yanmu iya mu'amala ta hanyar ba su tarbiyya ta gari.

Ba kowa ne zai dauki reni da harara ba ko da kuwa a haduwar titi ce.

Masu magana kan ce ka so naka, duniya ta ki shi....

Mu hadu a wani makon don jin faduwar bakar tasar da tarbiyyar samari 'yan bana bakwai ta yi.

Rahotun BBC Hausa

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN