Fitacciyar mawakiyar Pop na Afghanistan ta gudu zuwa kasar Turkiyya, duba abinda ya faru


Shahararriyar mawakiyar Pop na Afghanistan ta tsere daga kasar zuwa kasar Turkiyya sakamakon fargaba da ke bayyana kan makomar mata a kasar Afghanistan bayan Taliban ta kwace mulki kuma ta ce za ta sanya tsatsaurar Dokokin Shari'a a kasar. Shafin labarai na isyaku.com ya ruwaito.

Aryana Sayeed, mawakiya ce kuma Alƙali a The Voice, wani shirin auna fikirar fitattun mawakan Afghanistan, ta yi nassarar tserewa daga Afghanistan a cikin jirgin saman jigilan kaya na sojin Amurka zuwa kasar Turkiyya ranar Laraba 18 ga watan Agusta.

 Ta wallafa a shafinta na Instagram mai mabiya 1.3m cewa "Na isa gida Istanbul lafiya kalau bayan fama da radadin kunci na yan kwanaki. Yanzu na natsu kuma Ina lafiya kalau cikin kwanciyar hankali".
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari