Type Here to Get Search Results !

Dole ne a bankaɗo masu 'kisan Musulmi a Jos da Kudancin Kaduna


Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar Musulunci a Najeriya, Supreme Council for Shari'a in Nigeria, ta buƙaci gwamnatin tarayyar ƙasar da ta gaggauta hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen kisan Musulmai matafiya a jihar Filato a makon jiya. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.

A wani taron manema labarai a Kaduna ranar Juma'a, majalisar ta nuna damuwa kan wasu shugabanni wadanda ta yi zargin cewa su ne suke ƙulla maƙarƙashiyar tashe-tashen hankula musamman a jihohin Filato da Kaduna.

Sakataren majalisar ta NSCIA, Dr Nafi'u Baba Ahmad, ya faɗa wa BBC cewa sun gaji da gafara sa ba su ga ƙaho ba.

A cewarsa "kashe-kashen da a ke yi wa Musulmi a jihar Filato da yankin Kudancin Kaduna ya kai iyaka.

"Kullum hukumomi cewa suke yi za su ɗauki matakai, za su hukunta waɗanda suka aikata aika-aika amma ba abin da a ke yi."

Ya kara da cewa hakan ne yake ƙarfafa waɗansu su aikata ta'addanci saboda wasu sun yi babu abin da a ka yi musu.

Ba ya ga sama da Musulmi 20 ɗin da aka kashe a yankin Jos, NSCIA ta kuma bayar da misali da kisan Janar IM Alkali, wani babban jami'in sojin Najeriya, a yankin na Jos amma har yanzu babu abinda gwamnatoci suka yi.

NSCIA ta kuma yi jan kunne cewa matsawar hukumomin ba su hukunta masu kashe-kashe a jihohin Filato da kuma Kudanci Kaduna ba, wata rana abin zai fi ƙarfinta.

A makon jiya ne wasu matasa da ake zargin 'yan kabilar Iregwe ne suka kashe kusan mutum 30 tare da jikkata wasu da dama a Jos babban birnin Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya.

Waɗanda lamarin ya rutsa da su matafiya ne kuma Musulmai da ke kan hanyarsu ta zuwa Kudancin ƙasar daga Jihar Bauchi bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci.

Wasu mahara sun tare motocin da suke ciki a yankin Rukuba sannan suka rufe su da sara yayin da suke wucewa ta cikin birnin.

Kuma bayan faruwar lamarin ne gwamnatin jihar Filato ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomi uku - Jos ta Arewa da Jos Ta Kudu da kuma ƙaramar hukumar Bassa.

Kazalika tun a lokacin hukumomi a jihar suka tabbatar da kama sama da mutum 20.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Hollywood Movies