Da duminsa: Allah ya saukar wa Yan bindigan dajin Kaduna wani bala'i, duba abin da ya faru da su


Hukumomi a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu mambobin kungiyoyin 'yan bindiga da ke gaba da juna su tara sun rasa rayukansu sanadin musayar wuta a yankin ƙaramar hukumar Giwa.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rikicin ya faru ne a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar ta Giwa.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ya ce majiyoyin tsaro sun ba da rahoton cewa wani shahararren dan fashi da aka fi sani da 'Godon Mota' da yaransa sun abka wa kauyen Garke a ranar Larabar da ta gabata inda suka yi arangama da wata kungiyar' yan fashi da makami.

Ya ce lamarin da ya yi sanadin 'yan bindiga tara.

"Har yanzu ba a san musabbabin tashin hankalin ba amma an ce ya danganci rashin jituwa kan raba kudaden fansa, wanda a lokacin daya daga cikin kungiyoyin ya ji cewa an yaudare shi," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Mukaddashin Gwamna Dakta Hadiza Balarabe ta yi maraba da rahoton, sannan ta bukaci hukumomin tsaro da su ci gaba da matsa lamba kan cafke masu aikata laifuka a yankin baki daya."

Ba wannan ne karon farko da kungiyoyin 'yan fashin daji suke samun sabani a tsakaninsu ba lamarin da kan kai su ga hatsaniya.

Ko a watan Mayun da ya gabata rikici tsakanin 'yan bindigar da ke gaba da juna ya yi sanadin mutuwar Auwalu Daudawa, kasurgumin dan fashin dajin nan da ke da hannu wajen sace daliban sakandaren Kankara.

Kaduna na cikin jihohin da 'yan fashi a cikin daji ke tasiri inda su ke garkuwa da mutane da dama domin karbar kudin fansa.

Har yanzu akwai mutane da dama da suke garkuwa da su da suka haɗa da daliban makarantar sakandire ta Bethel Baptist da suka yi awon gaba da su a ƙaramar hukumar Chikun.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE