Bayan Yan Taliban sun kwace birane da dama, saura kilomita 11 su kwace Kabul babban birnin kasar Afghanistan


Wani ɗan majalisar dokoki ya shaida wa AFP cewa 'yan Taliban sun isa gundumar Char Asyab mai nisan kilomita 11 kacal daga kudancin babban birnin kasar, Kabul. BBC Hausa ta ruwaito.

Idan har gwamnati ta tabbatar da hakan, zai zama waje mafi kusa da birnin da suka kai kuma hakan babban koma-baya ne ga dakarun Afghanistan, wadanda ke yaki don hana Taluban shiga Kabul.

Dubban fararen hula sun tsere zuwa wajen danginsu a Kabul, babban birnin Afghanistan don samun mafaka, yayin da Taliban ke ƙwace iko da birane a kasar.

A yanzu masu tayar da kayar bayan suna kokarin shiga babban birnin, kuma wasu rahotanni na cewa jiragen yakin Amurka na kai hare-hare a inda 'yan Taliban suke a hanyoyin shiga gundumar Kabul.

Rahoton baya-bayan nan na leken asiri na Amurka ya nuna cewa Taliban za ta yi kokarin kutsawa birnin Kabul cikin kwana 30.

Kame birane da suke yi a kasar cikin mako guda da ya wuce na faruwa ne kamar kiftawar ido.

Ko a jiya Juma'a sai da Taliban ta kwace Pul-e-Alam, babban birnin yankin Loghar, mai nisan kilomita 80 daga Kabul.

A yanzu Taliban na iko da kusan rabin manyan biranen gundumomi bayan kwace muhimmai da suka hada da Kandahar, birni na biyu mafi girma a ƙasar. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE