Rundunar 'yan sandan Jihar Osun a kudancin Najeriya ta kori wani É—an sanda daga aiki bisa zargin kashe wani mutum a kan babur a garin Osogbo. Shafin BBC Hausa ya ruwaito.
Kamfanin labarai na NAN ya ruwaito cewa Saja Adamu Garba ya harbe wani mai suna Saheed Olabomi ranar 27 ga watan Yuli.
A cewar kakakin 'yan sandan jihar, SP Yemisi Opalola, an kori jam'in ne bayan gudanar da shari'ar cikin gida.
"Kamar yadda Kwamishinan 'Yan Sanda Olawale Olokode ya yi alƙawari za a bayyana sakamakon shari'ar...an yi wa F/NO.467549 Sergeant Adamu Garba shari'a bisa ƙa'idojin aikin ɗan sanda na Najeriya," a cewar wata sanarwa.
"An samu É—an sandan da laifin aikata zargin da ake yi masa kuma aka kore shi daga rundunar. An tura wa hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja hukuncin shari'ar domin É—aukar matakin gurfanar da shi a gaban kotu."
Kwamishinan ya ce yana fatan hukuncin zai zama darasi ga sauran 'yan sanda.