Ban hakura ba har yanzu musamman idan na gan Yara suna firgita saboda ganina


 A 2018 ne dai wasu mutane da ba a tantance su wanne ne ba suka shiga gidan su Amina Musa da tsakar dare suka watsa mata ruwan asid tare da mijinta ta taga. BBC Hausa ta ruwaito.

''Ni dai na farka da daddare sai na ji ruwa a fuskata mai sanyi, sai na ce da mai gidana ka ji wani abu mai sanyi? Asid ne'', In ji Amina.

Daga nan ne Amina da mijinta suka garzaya asibiti inda aka kwantar ta ita har tsawon wata bakwai.

To sai dai Amina ba ta koma yadda take ba kasancewar kudin da ake nema domin yi mata aiki ba su samu ba.

'Ana neman dala 23,000 kwatankwacin naira miliyan tara to amma naira miliyan biyu kawai aka iya samu kuma dalibai ne suka hada kudin.

Saboda ganin kudin ba su isa ba sai kawai na jefa su a harkar kasuwancin da nake yi wato sana'ar sayar da kayan kicin."

Yanzu dai burin Amina shi ne samun zarafin da za ta fita kasar waje a yi mata wannan aiki domin samun saukin halin da take ciki duk da cewa dai fuskarta ba za ta taba komawa kamar da ba.

"Ban hakura ba har yanzu saboda abin na damu na musamman idan na ga kananan yara suna firgita saboda gani na."


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE