Tsadar kayan abinci: 'Ƴan Najeriya za su ci gaba da ɗanɗana tsadar rayuwa'


Masana tattalin arziki a Najeriya na gargaɗin cewa zai yi matukar wuya a iya cimma hasashen nan da babban bankin kasar CBN ya yi, cewa hauhawar farashin kaya da ake fama da ita a kasar za ta sauka. BBC Hausa ta ruwaito.

Shi dai bankin ya yi hasashen cewa nan da shekarar 2022 farashin kayan abinci zai sauka da kashi goma cikin dari, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da kuma rashin bin matakan da suka kamata.

Kasimu Garba Kurfi, wani masanin tattalin arziki da ke birnin Legas, yana cikin masu irin wannan ra'ayi, kuma ya shaida wa BBC cewa matsawar mahukunta ba su tashi tsaye wajen daukar matakin da ya kamata ba, lamarin zai ci gaba da dagulewa ne maimakon ya gyaru.

"Abu ne mai wuya a iya samun wani cigaba, saboda halin da muka samu kanmu, ga rashin aikin yi, ga matsalar tsaro an kasa magance ta, don haka dukkan wadannan matsaloli akwaisu, kuma baza su bada damar haifar da wani sauyi ba" in ji masanin.

Ya ƙara da cewa "abun da gwamnati ya kamata ta yi shi ne ta fadada hanyoyin samun kudi, domin ta iya aiwatar da manufofinta na yau da kullum, sannan a samar da zaman lafiya don in akwai shi to mutane za su iya fita su nemi na kansu".

A baya bayan nan ne Bankin Duniya ya ba da rahoton cewa sama da mutum miliyan bakwai sun sake faɗawa talauci a bara kawai saboda ƙaruwar hauhawar farashi a Najeriya.

Bankin ya ce a cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.

Rahoton na Bankin Duniyar ya yi nuni da abin da ya kira da fitattun garanbawul na gwamnati, da nufin shawon kan tasirin anobar cutar korona da kuma tallafawa wajen farfado da tattalin arziki, cikin su har da matakan rage tallafin man fetur, da daidata farashin wutar lantarki.

Dukkansu kuma in ji rahoton don bunkasa kafofin samun kudin shiga da nufin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar talaka ne. 

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN

Latsa nan domin samun labaran mu ta WhatsApp kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilin mu a garin ku LATSA NAN

Domin aiko rahotu/ korafi LATSA NAN

Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN ka danna FOLLOW ko LIKE