Shahararren malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya yi hasashen cewa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki za ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023.
Ayodele ya fadi haka ne a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, inda ya ce hasashensa zai zama gaskiya idan ba a magance matsalar rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan ba.
Malamin ya ce 'yan Najeriya sun gaji da jam'iyya mai mulki kuma suna bukatar gyara duk dimbin kalubalen da kasar ke fuskanta, jaridar PM News ta ruwaito.
Ya kuma yi hasashen cewa talakawa za su yi tawaye kan magudin zabe a 2023 kamar yadda ya gaya wa jam'iyyar da ta yi hanzarin daukar mataki.
Malamin ya fadawa shugabannin APC da su magance matsalolin shari’a da jam’iyyar ke fuskanta domin kada a sauke su daga kujerar shugaban kasa bayan zaben 2023.
A zaben da ke tafe a Anambra, Primate Ayodele ya tsaya tsayin daka kan maganarsa cewa jam’iyya mai mulki ba za ta yi nasara ba, jaridar Daily Post ta ruwaito.
Source: Legit