Mutum 260 sun kamu, 23 sun mutu sakamakon bullar cutar muran hanji a jihar Sokoto


Mutum 23 sun mutu sakamakon bullar wata cuta dake kama tunbin mutum dama sauran magudanun abinci, wacce kuma take janyo gudawa da amai a wasu sassan jihar Sokoto.


Shafin isyaku.com ya lruwaito cewa, Kwamishinan lafiya na jihar Sokoto Mohammed Iname, ya sanar da haka ranar Talata 3 ga watan Agusta.

Ya ce mutum 260 daga 13 cikin kananan hukumomi 23 sun kamu da cutar a jihar Sokoto.

Ya ce kananan hukumomi da lamarin ya fi shafa sun hada da Dange/Shuni, Kebne, Gwadabawa, Tangaza, Isa, Bodinga, Wamakko, da Silame.

Ya ce karamar hukumar Gwadabawa ke da yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar har mutum 47.

Ya kuma gargadi jama'a cewa su yi taka tsan tsan tare da kulawa saboda cutar tana yaduwa da sauri a cikin jama'a.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN