Allah ya tona asirin saurayin da ke taushe tsofaffin mata ya yi masu fyade a gonakinsu


Jami'an tsaro sun kama wani Manomi mai suna Steven John wanda ya shahara wajen yi wa tsoffin mata da yan mata fyade a gonakinsu.

Stephen John, ya gaya wa yansanda cewa yana fakewa da cewa yana aiki a gona, sai ya sami tsofaffin mata ko yan mata a gonakinsu ya yi masu fyade a Ore, da ke rikon Odigbo a jihar Ondo.

Dubun Steven ta cika ne bayan ya tare wata yarinya mai suna Fatima Yahaya bayan mahifiyarta ta aike ta. Steven ya sharbe ta a kan hany ya jayeta zuwa cikin jeji ya yi mata fyade da karfin tsiya.

Yanzu haka Steven na hannun yansanda yana fuskantar bincike bayan mahaifiyart Fatima ta kai kararsa wajen yansanda. 


Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN