An kama wani Bafulatani dauke da albarussan bindiga guda 200 a hanyarsa ta zuwa garin Jos a jihar Plateau kan babur (Hotuna)


Jami'an tsaro a jihar Nassarawa da ke tsakiyar Najeriya, sun cafke wani Bafulatani mai suna Likta dauke da abarussan bindiga guda 200 kan hanyarsa ta zuwa garin Jos a jihar Plateau. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Penexpress ta wallafa cewa jami'an yansandan garin Akwanga tare da hadin gwiwa da jami'an FRSC da suke sintiri tare, sun kama Likita dauke da albarussan a kan babur da yake tukawa kan hanyarsa ta zuwa Birnin Jos.

Rahotanni sun ce Likita yana tare da wasu Fulani su shida, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Jos kafin a kama shi.

Yanzu haka yana tsare a nannun jami'an tsaro yana fuskantar bincike. Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari