Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa wata Kotun Shari'ar Musulunci da ke birnin Kano a arewacin Najeriya tana can ta soma shari'ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.
Jami'an gidan gyaran hali ne suka kai malamin kotu da safiyar Laraba domin a soma shari'arsa a kotun wadda mai shari'a Ibrahim Sarki Yola yake jagoranta.
Ranar Juma'a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin ɓatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.
Wakilin BBC da yanzu haka yake kotun ta Kofar Kudu a birnin Kano ya ce da alama Sheikh Abduljabbar yana cikin koshin lafiya sai dai ya dan rame.
Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin da wanda ake kara ke tsayawa.
Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.
A bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da Yahuza mohd Nura da Bashir Sabi'u, RS Abdullahi, Y I Abubakar, Zaubairu Abubakar, Ya'u Abdullahi Umar, B S Ahmad, da kuma Umar Usman.