Kotu ta saki Ibrahim El-Zakzaky jagoran IMN da matarsa Zeenat


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenat, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waÉ—anda ake zargin a ranar Laraba daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

"Kotun ta sallame su ne saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja," a cewarsa.

Wakilin BBC a Kaduna Yusuf Tijjani ya ce jim kaɗan bayan bayar da hukuncin ne aka fita da jagoran na ƙungiyar 'yan Shi'a ta Islamic Movement in Nigeria (IMN) a mota zuwa gida, inda ba su saurari ko 'yan jarida ba.

Motar da Zakzaky ke ciki bayan sakinsa
Bayanan hoto,

Wasu 'yan jarida sun yi nasarar É—aukar hoton motar da ta É—auki Sheikh El-Zakzaky zuwa gida yayin da ta fito a guje

Barista Sadau ya ƙara da cewa kotu ta yi tsokaci kan cewa "ta yaya za a zargi mutum da aikata laifi a 2015 sannan kuma a tuhume shi da dokar da aka samar a 2017".

An gudanar da zaman shari'ar na ranar Laraba ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Gideon Kurada a asirce yayin da aka hana kowa shiga farfajiyar kotun balle ma ɗaƙin da ake gudanar da ita.'


Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba kan ko za ta ɗaukaka ƙara.

Tun a shekarar 2015 ne aka kama Sheikh Zakzaky bayan mabiyansa sun yi arangama da dakarun sojan Najeriya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Mabiyan nasa sun sha hawa tituna domin neman a saki jagoransu, inda suka dinga yin arangama da jami'an tsaro musamman a Abuja, babban birnin ƙasar.

A watan Yunin 2020 wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci 'yan sandan su biya Æ™ungiyar IMN mabiya Shaikh Ibrahim El-zakzaky naira miliyan 15 saboda kisan mambobinta uku yayin wata zanga-zanga a Abuja.

Gaskiya da adalci sun yi nasara a kan zalunci - IMN

Ƙungiyar IMN ta mabiya Shi'a wadda Sheikh El-Zakzaky ke jagoranta ta bayyana hukuncin kotun da cewa "nasara ce a kan gwamnatin Najeriya".

Cikin wata sanarwa da kakakinta Ibrahim Musa ya aike wa BBC Hausa, IMN ta ce hukuncin ba iya Zakzakya da matarsa kaɗai ya wanke ba "har da dukkan 'ya'yan ƙungiyar IMN".

"Shari'ar ba wai su kaɗai da kuma sauran 'yan IMN ta wanke ba, tabbas nasara ce wadda haƙuri ya haifar yayin da gwamnatin Najeriya ke gallaza [mana]," a cewarsa.

Ya ƙara da cewa "gaskiya da adalci sun yi nasara a kan kama-karya da zalunci".

Tarihin abubuwan da suka faru da El-Zakzaky da mabiyansa tun bayan tsare shi

Tarihin arangamar 'yan Shi'a da jami'an tsaro da zanga-zanga da kuma shari'ar da ake yi wa jagoran kungiyar Islamic Movement In Nigeria, Ibraheem Zakzaky.
  •  
    1980s
    Sheikh Ibrahim Zakzaky ne ya kafa Islamic Movement In Nigeria(IMN)
  •  
    Yuli 25, 2014
    Rahotanni sun ce an sojojin sun kashe mabiyan El-zakzaky guda 35 lokacin tattakin ranar Qudus a Zariya da ke jihar Kaduna. Uku daga cikin wadanda aka kashe 'ya'yan Zakzaky ne.
  •  
    Disamba 12, 2014
    Sojoji sun yi zargin daruruwan mabiyan Islamic Movement In Nigeria da tsare wa hafsan sojin kasar, Laftanar Janar Tukur Burutai, hanya a kan titin Sokoto road da ke Zaria, inda sojoji suka yi zargin kungiyar da yunkurin kashe Buratai, duk da kungiyar ta musanta.
  •  
    Disamba 12-13, 2014
    An zargi sojojin Najeriya da kashe 'yan Shi'a 300 kuma suka binne gawarwakinsu. Sojojin sun musanta.
  •  
    Disamba 14, 2014
    -
  •  
    Nuwamba 14, 2016
    An kashe 'yan Shi'a takwas da dan sanda guda yayin wata arangama a lokacin wani tatttaki a birnin Kano. 'Yan sanda sun hana 'yan Shi'a yin tattaki daga Kano zuwa Zaria domin halartar ranar Ashura.Majalisar Koli ta Musulmi(NSCIA) ta ziyarci Sheikh Zakzaky a Abuja.
  •  
    Disamba 2, 2016
    Wata babbar kotu a Najeriya ta ba da umarnci hukumar SSS da ta saki Elzakzaky a cikin kwana 45.
  •  
    Janairu 20, 2017
    Kotun ta ce idan ba a bi umarninta ba to za ta kama sifeto janar na 'yan sanda na wancan lokaci, Ibrahim Idris da ministan Shari'a, Abubakar Malami da Darakta Janar na SSS, Lawal Daura, da laifin rasahin girmama kotu kuma za su iya fuskantar zaman gidan kaso idan suka ci gaba da yin burus da umarnin na kotu na Disamba 2, 2016.
  •  
    Janairu 7, 2018
    Jmai'an tsaro sun kashe dalibai guda biyu a lokacin zanga-zangar neman a saki Elzakzaky a Kaduna d ake arewacin Najeriya.Duk da umarnin da babbar kotun ta bayar da a saki Zakzaky, amma yana tsare a hannun SSS a wani boyayyen wuri. Gwamnati ta sha ikrarin cewa ba ta da hurumin sakin Zakzaky saboda shari'ar da ke masa tana hannun kotu a jihar Kaduna. Hakan ne ya sa mabiya IMN suka lashi takobin ci gaba da zanga-zanga har sai an saki jagoran nasu ko da kuwa za su kare baki dayansu.
  •  
    Janairu 13, 2018
    Shugaban IMN, Sheikh Zakzaky ya bayyana a karon farko tun bayan kama shi, inda ya ce ya yi fama da bugun jini maras tsanani a ranar 5 ga Janairu. Zakzaky wanda yake sanye da wani abun wuya ya ce a karon farko an bar shi ya ga likitocinsa bayan da ya nace.
  •  
    Afrilu 16, 2018
    Yan sanda sun yi rikici da 'yan IMN a lokaci wata zanga-zangar neman sakin Zakzaky a dandalin Unity Fountain, Abuja inda aka kashe mutum daya sannan da dama suka jikkata.
  •  
    Afrilu 23, 2018
    Yan Shi'a sun sake haduwa da fushin 'yan sanda lokacin wani tattaki zuwa hukumar kare hakkin dan adam. An kama 'yan IMN akalla 115.
  •  
    Mayu 15, 2018
    An gurfanar da Elzakzaky da matarsa Zeenat a gaban mai shari'a, Gideon Kurada na babbar kotu da ke Kaduna bisa tuhume-tuhumen kisan kai da taro ba da izni ba  da kuma tayar da zaune tsaye da dai sauransu. Gwamnatin jihar Kaduna ce ta shigar da karar.
  •  
    Yili 11, 2018
    Kotu ta dage karar zuwa 2 ga Agusta 2018
  •  
    Agusta 2, 2018
    Kotu ta dage bukatar Elzakzaky ta neman beli zuwa Oktoba 4, 2018
  •  
    Oktoba 4, 2018
    Alkali ya sake dage sauraron bukatar bayar da belin Zakzaky zuwa Nuwamba 17, 2018.
  •  
    Oktoba 27, 2018
    Mbaiya Zakzaky sun yi dandazo a gadar Zuba da ke Abuja. Sun yi taho-mu-gama da tawagar sojoji da ke daukar makamai, al'amarin da ya janyo kashe 'yan Shi'a guda uku.
  •  
    Oktoba 29, 2018
    An sake samun arangama tsakanin 'yan Shi'a da sojoji da 'yan sanda. Sojojin sun fadi cewa an kashe 'yan Shi'a guda uku duk da cewa 'yan Shi'ar sun ce mutum kusan 50 sojojin suka kashe.
  •  
    Oktoba 30, 2018
    Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 400 bisa tuhumar tayar da zaune tsaye a Abuja. Jmai'an tsaro sun zargin 'yan Shi'ar da mallakar bam din da ake yi fetir guda 31 da sauran muggan makamai. Sojoji sun ce mutum uku ne suka mutu amma IMN ta ce gwammai ne.
  •  
    Nuwamba 17, 2018
    Kotu ta yi watsi da bukatar neman beli bisa dogaro da cewa babu wata sheda daga likitoci da ke nuna bukatar belin domin neman lafiya.
  •  
    Disamba 7, 2018
    Daruruwan magoya bayan Zakzaky sun hau titunan Abuja suna zanga-zangar neman a saki jagoransu.
  •  
    January 22, 2019
    Mai shari'a Gideon Kurada ya yanke cewa hukumar DSS ta ci gaba da tsare Zakzaky da mai dakinsa, Zeenat sannan a ba shi damar ganin likitoci.
  •  
    Yuni 29, 2019
    Mai shari'a Kurada ya dage karar ba tare da sanya wata rana ba saboda zai shiga sahun alkalan kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da 'yan majalisa a jihar Yobe.
  •  
    Yuli 9, 2019
    Yan sanda da 'yan Shi'a sun sake taho mu-gama a wajen majalisar dokokin Najeriya. 'Yan sanda sun ce an harbi jami'ansu guda biyu a kafa sannan an jikkata wasu guda shida da duwatsu. 'Yan sanda sun kama 'yan Shi'a 40. Sai dai wani mamban kungiyar Abdullahi Muhammad Musa ya shaida wa Reuters cewa 'yan sanda sun bude musu wuta, inda suka kashe masu zanga-zanga biyu a lokacin da suke kokairn shiga majalisar dokoki cikin ruwan sanyi.
  •  
    Yuli 10, 2019
    Yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki El-zakzaky kamar yadda kotuna da dama suka yi umarni.
  •  
    Yuli 18, 2019
    Mai shari'a D.H Khobo ta jagoranci zaman sauraron bukatar neman beli wadda aka dage zuwa 29 ga Yuli 2019. Ta ce "Yana da muhimmanci a fahimci cewa gwamnatin tarayya ba ta da hannu a ci gaba da rike da Zakzaky kasancewar shari'ar da ake yi masa ta koma hannun jiha. Ba kasafai ake bayar da belin mutumin da ake zargi da kisa ba abin da ya sa Elzakzaky da mai dakinsa ke dogara da batun neman lafiya."
  •  
    Yuli 22, 2019
    Mataimakin kwmaishinan 'yan sanda, Umar Umar da dan jaridar gidan talbijin na Channels, Precious Awolabi da wasu 'yan kungiyar IMN 11 sun rasa rayukansu a rikici tsakanin jami'an tsaro da 'yan Shia lokacin wata zanga-zanga a Abuja.
  •  
    Yuli 26, 2019
    Gwamnati ta samu hukuncin babbar kotu a Abuja na haramta ayyukan 'yan Shi'a mabiya Zakzaky.
  •  
    Yuli 29, 2019
    Mai shari'a Darius Khobo ta babbar kotun jihar Kaduna ta dage sauraron bukatar Zakzaky da mai dakinsa ta zuwa India neman magani zuwa 5 ga Agusta. Sheikh Zakzaky bai je kotun ba.
  •  
    Yuli 31, 2019
    IMN ta sanar da dakatar da zanga-zanga domin bin wasu sabbin hanyoyin warware rikicin da kuma kai gwamnatin tarayya kara a kotu kan haramta ta.
Tarihi daga Azeezat Olaoluwa da Princess Abumere da Olawale Malomo.
Hakkin Mallaka na hoto: Getty Images.

Yadda Shi'a take a Najeriya

Mabiya Shi'a a Najeriya

ASALIN HOTON,AFP

  • Yan Shi'a tsiraru ne a Najeriya, amma rahotanni na nuna cewa yawansu na karuwa
  • Kungiyar IMN, wadda aka kafa a shekarun 1980, ita ce babbar kungiyar 'yan Shi'a wadda Ibraheem Zakzaky ke jagoranta
  • Tana gudanar da makarantu da asibitocinta a wasu jihohin arewacin kasar
  • Kungiyar tana da tarihin arangama da jami'an tsaro
  • IMN tana samun goyon bayan Iran inda 'yan Shi'a suke da rinjaye, kuma 'yan kungiyar na yawan zuwa Iran karatu
  • Kungiyar Boko Haram da ke ikirarin bin mazhabin Sunna tana kallon 'yan Shi'a a matsayin fandararru, kuma ta sha kai musu hari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN