Yanzu yanzu: An soma shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara a Kano


Shafin BBC Hausa ya ruwaito cewa wata Kotun Shari'ar Musulunci da ke birnin Kano a arewacin Najeriya tana can ta soma shari'ar malamin nan na jihar Sheikh Abduljabbar Kabara.

Jami'an gidan gyaran hali ne suka kai malamin kotu da safiyar Laraba domin a soma shari'arsa a kotun wadda mai shari'a Ibrahim Sarki Yola yake jagoranta.

Ranar Juma'a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin …ďatanci ga addini da kuma tunzura jama'a, zargin da ya sha musantawa.

Wakilin BBC da yanzu haka yake kotun ta Kofar Kudu a birnin Kano ya ce da alama Sheikh Abduljabbar yana cikin koshin lafiya sai dai ya dan rame.

Alkali Sarki Yola ya bayar da umarnin a shiga da Sheikh Albduljabbar cikin akwatin da wanda ake kara ke tsayawa.

Aisha Mahmud ita ce ke jagorantar lauyoyin gwamnatin Kano.

A bangaren Sheikh Abduljabbar, lauyoyinsa sun hada da Sale Mohammad Bakaro, da Yahuza mohd Nura da Bashir Sabi'u, RS Abdullahi, Y I Abubakar, Zaubairu Abubakar, Ya'u Abdullahi Umar, B S Ahmad, da kuma Umar Usman.

Previous Post Next Post

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN