Yadda gwamnatin Katsina ta sanya wa mutane da dabbobi haraji da jangali


Gwamnatin Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wata sabuwar doka da ta janyo ce-ce-ku-ce a jihar da za ta tursasa wa jama'a fara biyan haraji da zummar tara kudaden da za a yi musu ayukan more rayuwa da su.

Sabuwar dokar haraji da jangalin ta bukaci daga yanzu kowanne dan jihar da ya mallaki hankalinsa zai rika bai wa gwamnati wani kashi na abin da yake samu a kowacce shekara.

Dokar ta yi tanadin cewa duk wani mazaunin jihar, daga kan ɗan shekara 18 zuwa sama, zai riƙa biyan Naira dubu biyu (2000) a matsayin harajin raya ƙasa, yayin da za a riƙa biyan Naira ɗari biyar (500) ga duk wata saniya da ake kiwo a shekara.

Dokar ta sassauta wa mata inda su kuma sai macen da ke da aikin yi ce kadai za ta biya Naira dubu biyu (2000) a shekara.

Kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki na jihar Katsinar Faruk Lawan Jobe, ya bayyana wa BBC Hausa cewa akwai kasashe da dama da suka fi Najeriya talauci, amma hakan bai hana su karbar haraji daga jama'a ba.

''Naira dubu biyu ai ba za a ce ta yi yawa ba a shekara, sau daya kacal fa, kasashen Turawa su kansu ginshikin tattalin arzikinsu ya ginu ne a kan harajin da mutane ke bayarwa'' a cewarsa.

Tuni dai wasu daga cikin al'ummar jihar suka fara bayyana ra'ayoyi masu karo da juna dangane da wannan mataki na gwamnatin jihar da masu sharhi ke ganin cewa jama'a za su turje masa.

A yayin da wasu ke ganin cewa matakin ya yi daidai musamman a yayin da tattalin arzikin kasar ya fada halin ni-'ya-su sanadin annobar korona, wasu kuwa na ganin cewa bai kamata gwamnatin ta bijiro da wannan doka a yayin da yawancin mutane ba ma sa iya rike kansu ba, ballantana su biya harajin.

Raguwar kuɗin shiga da gwamnatocin Nijeriya ke fama da ita sakamakon karyewar farashin man fetur da cutar korona ta haddasa, ta sa su neman wasu hanyoyi domin bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗe.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN