Bayan shekara 45 yana mulki, Allah's ya yi wa wani basarake mai daraja ta 1 rasuwa a Arewa


Sarkin Lafiagi, Alhaji Saadu Kawu Haliru ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun ce basaraken ya rasu ne a wani asibiti a Abuja misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Alhamis.

Sarki mai daraja ta É—aya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Sarki mai daraja ta É—aya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki. Hoto: Daily Trust

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa za a kai ganawarsa jihar Kwara a ranar Juma'a zuwa Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu inda za a yi masa jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Marigayi Sarkin Lafiagi, sarki ne mai sanda mai daraja ta É—aya wanda ya hau mulki. 1975 kuma ya yi bikin cika shekaru 45 kan mulki a ranar 21 ga watan Oktoban 2020.

Da ya ke tabbatar da rasuwar, Ndegi na Lafiagi, Alhaji Ahmed Kaiama, ɗaya daga cikin masu zaɓen sarki ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasar Nupe.

Marigayin ne shugaban majalisar gidan Radio Kwara.

Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyyar rasuwar Sarkin

A sakonsa na ta'aziyya, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya bayyana Marigayin Sarkin a matsayin mai kira ga zaman lafiya da hadin kai kuma rasuwarsa ya kawo ƙarshen wani zamani mai daraja.

Abdulrazaq ya ce:

"Sarkin mai daraja ta É—aya mutum ne mai baiwar basira ta sarauta, tausayi da zaman lafiya. Ya kasance yana kira ga zaman lafiya da haÉ—in kai duk da banbancin da ke tsakanin mutane, hakan yasa aka samu gagarumin cigaba a zamanin sarautars."

"Rasuwar mai martaba ta kawo karshen wani muhimmin shafi a tarihi, duba da cewa shi ya jagoranci farfaÉ—o da al'adu da inganta rayuwar al'ummarsa tsawon shekaru 45 da suka shuÉ—e."

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta gabatar da tsarin amsar kudin bunkasa jihar da kuma jangalin shanu.

Alhaji Faruk Jobe, kwamishinan kasafi da tattalin jihar ne ya bayyana hakan a ranar Laraba bayan wani taro na masu ruwa da tsakin jihar wanda gwamna Aminu Masari ya shirya.

Legit hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN