Yadda kalaman Sarkin Muri kan Fulani Makiyaya suka ta da ƙura


A jihar Taraba a Najeriya jama'a na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu ga wasu kalaman da Sarkin Muri Abbas Tafida dangane da fulanin da ke dazukan jihar. BBC Hausa ta wallafa.

A shekaran jiya Talata ne basaraken cikin jawabinsa na sallah, ya bai wa fulani makiyaya wa'adin kwanaki 30 na su bar dazukan jihar ko kuma su daina garkuwa da mutane.

Cikin kakkausan lafazi kuma a fusace Mai Martaba Sarkin Muri Abbas Tafida ya ce duk da cewa su ma Fulani ne kamar su amma ba za su zura ido ba mazauna dajin na yi musu dauki dai-dai.

Jawabin Sarkin dai tsumagiyar kan hanya ce don bai tsaya kan Fulani dajin ba.

Ƙoƙarin da BBC ta yi na jin tunanin gwamnatin jihar ta Taraba dangane da wannan wa'adin Sarkin na Muri ya bayar dai bai yi nasara ba.

Haka ma ita ma kungiyar Fulani Makiyaya ta Kasar Miyetti Allah- wadda a mafi yawan lokutta ke yin wuf, ta kare Fulani daga irin wannan zargin ta ce ba za ta ce komai ba game da kalaman Sarkin.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari