Wata mata ta shawarci ’yan uwanta mata da su dafa wa mazajensu yayin da za su kara aure


Wata mace Musulma 'yar kasar Kenya ta bukaci mata da su tallafa wa mazajensu idan sun yanke shawarar auren mace ta biyu.

Matar tana magana ne da 'yan uwanta mata ta hanyar bidiyon TikTok wanda aka yada ta mai amfani da sunan @nps254 kuma tun daga lokacin bidiyon ya karade shafukan intanet.

Ta ce mata su daina fada da maza saboda auren mace fiye da daya abu ne na al'ada.

Ta ce:

"Idan iyayensa ba su yi fada a kansa ba, to ku a wa za ku yi fada a kansa, namiji mai aure? Don haka lokacin da mutum ya yanke shawarar yana son kara aure, kawai yi masa addu'ar ya samu mata ta gari wacce za ku taimaki juna."

Matar 'yar kasar ta Kenya da ba a san ko wacce ce ba, ta ce lokaci ya yi da mata za su daina fada da juna a kan maza kuma maimakon haka su karkata zuwa fada a kan ilimi da aiki da samun karin girma da ci gaba da ma sauran ababuwa masu kyau.

Wata mata ta shawarci ’yan uwanta mata da su dafa wa mazajensu yayin da za su kara aure

Wata mata ta shawarci ’yan uwanta mata da su dafa wa mazajensu yayin da za su kara aure Hoto: @Nps254/TikTok

Ta kara da cewa:

"Auren mace fiye da daya yana nan, ko mun yarda da shi ko mun ki shi ko mun musanta shi. Amma fa yana nan daram. Ko mazajen Kirista ma ya kamata su daina boyewa suna komawa gida wurin matansu, amma a gefe suna da farkar da suka boye a wani wurin. Wannan ba shi ne mafita ba. Ku gabatar da su kuma ku sanar musu da junansu."

Galibin mazan da suka yi tsokaci sun na’am da ra'ayinta inda suka nemi matan da su daina nuku-nuku a kan batun auren mace fiye da daya muddin dai mijin nasu yana adalci tsakaninsu.

Sai dai wadansu mata sun dage cewa aure ya kasance tsakanin namiji daya da mace guda kawai kuma auren mace fiye da daya yana dagula iyalai.

Wata mata ta amince da kishiyarta da mijinta ya aura

Legit.ng ta ruwaito a baya cewa wata mata mai amfani da @belllahijabi ta janyo hankalin mutane a shafukan sada zumunta bayan ta zo ta sanar cewa mijinta ya auri mata ta biyu.

A cikin sautin da aka jiyo ta tana cikin matukar farin ciki, ta ce ta fi mijinta farin ciki game da wannan ci gaban da ya samu.

Matar da ta kasance tagari ta yi addu'ar Allah Ya kara bai wa iyalinsu sa'a da kariya daga zafin kishi wanda zai iya haifar da sabani da rashin jituwa.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN