-->

Ads

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, LauyansaYa ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Ya ce:

"Sun ɗaure shi da mari a inda aka ajiye shi a Cotonou. Anyi hayaniya a filin tashin jiragen sama a lokacin da aka kama shi. Sun buge shi a hannu sannan suka saka masa ankwa a hannun, yana cikin azaba kuma yana ta sharɓar kuka tamkar yaro ƙarami a lokacin da na kira shi, na ji shi.

"Ita ma matarsa an saka ta a wani ɗaki daban amma ba a saka mata mari ba, ita ma matar tana kuka saboda yana cikin azaba. Muna addu'ar kada su biya wani ya kashe shi. Ba daidai bane ka rufe mutum sannan ka saka masa mari.

"Kun san ya ji ciwo amma ba ku kai shi asibiti ba. Mun ji cewar za a gurfanar da shi a kotu gobe ba mu san ko hakan zai yiwu ba."

Idan za a iya tunawa dai an kama Igboho da matarsa ne a filin tashin jirage na Cadjehoun, Jamhuriyar Benin misalin ƙarfe 8 na daren ranar Litinin. Suna shirin shiga jirgi zuwa Jamus kafin yan sandan kasa da kasa suka kama su.

Rahotanni sun ce jakadar Nigeria a Jamhuriyar Benin, Laftanant Janar Tukur Buratai (mai murabus) yana kokarin ganin an dawo da Igboho da matarsa Nigeria.

Bai dace a mika wa gwamnatin Nigeria Igbobo ba

Amma Aliyu ya ce yarjejeniyar mayar da masu laifi kasashensu ta 1984 da Togo, Ghana, Nigeria da Jamhuriyar Benin suka rattaba hannu a kai ta bawa wadanda suka baro kasarsu saboda dalilan siyasa kariya. Ta kuma ce kada a mayar da wanda ake zargin ƙasarsa idan akwai yiwuwar ba za a yi masa adalci ba.

Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.

Legit Hausa

0 Response to "Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa "

Post a Comment

Rubuta ra ayin ka

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN