Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC


Jam'iyyar APC ta bayyana cewa a lokacin da ya dace, zata fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na 2023 wanda kowa zai amince da shi, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Sakataren kwamitin riƙon kwarya na jam'iyya mai mulki, Sen. John Akpanudoehede, shine ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Jawabin ya yi martani ne game da zargin da PDP ta yi cewa shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya na son cigaba da mulki.

Sakataren APC ya jaddada cewa jam'iyya ba zata bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin shugaba Buhari yadda suke so ba, a dai dai lokacin da zaɓen 2023 ke gabatowa, kamar yadda the nation ta ruwaito.

APC ta sha Alwashin fitar da É—an takara nagari a 2023

Da Duminsa: Zamu Fitar da Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023 Wanda Kowa Zai Kaunace Shi, APC Hoto: channelstv.com

Zamu baiwa PDP mamaki

A cewar sakataren APC, bayan jam'iyyarsu ta yi gangamin ta na ƙasa zata baiwa jam'iyyar adawa PDP mamaki.

Yace: "Bayan babban taron mu na ƙasa, zamu basu mamaki (PDP) idan muka fitar da amintaccen ɗan takarar shugaban ƙasa kuma kowa ya amince da shi, wanda zai ɗaga tutar APC a zaɓen 2023."

"APC ba ta da kudirin zarcewa zango na uku a kan mulki kamar PDP, abinɗa muke yi yanzun shine ƙara kafa jam'iyya kuma ba zamu bar wasu ɗai-ɗaikun mutane su dinga juya gwamnatin mu ba."

Bamu da kuduri irin na PDP

Sakataren APC ya ƙara da cewa jam'iyyarsu ba kamar PDP bace domin yanzun PDP tana girban abinda ta shuka a baya ne.

Akpanudoedehe ya tuna cewa PDP ta so zarce wa a kan karagar mulki zango na uku lokacin da mulki ke hannunta.

A cewarsa, APC ba ta da wannan shirin, kuma zata ba PDP mamaki idan ta kammala babban gangaminta na ƙasa wanda aka shirya farawa ranar 31 ga watan Yuli.

Shugaban ƙasa, Buhari, ya nuna rashin jin daɗinsa da hatsarin jirgin yaƙin NAF a jihar Zamfara.

Buhari, wanda aka bashi labarin lamarin da ya faru a mahaifarsa Daura, yace ya kaÉ—u sosai da jin labarin.

Source: Legit.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN