Mutane miliyan 7 na bukatar taimakon jin kai a arewa maso-gabashin Najeriya


Sakamakon ta'addancin kungiyar Boko Haram, mutane miliyan 7 ne ke bukatar taimakon jin kai a arewa maso-gabashin Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito Mai Bawa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha'anin Tsaro Babagana Monguno na jawabi a wajen Karo na Biyu na Taron Hukumomin Yaki Ta'addanci a Kasashe Mambobin Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar.

A jawabin nasa, Monguno ya shaida cewa, ta'addanci na ci gaba da yin barazana ga duniya ba tare da nuna bambancin kasa, launin fata, yare ko addini ba.

Monguno ya kara da cewa, ta'addanci a lokacin hadewar duniya waje guda ya zama wani babban makami da ake amfani da shi ga wasu mutane, kuma a yanzu akwai mutane miliyan 7 da ke bukatar taimakon jin kai a arewa maso-gabashin Najeriya.

Ya ce, "Baya da annoba, ibtila'o'i da sauyin yanayi, ta'addanci ne babban makiyin dan adam da ke yi masa barazanar wanzuwa."

Rahotun TRT

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN