-->
An gano yadda aka yiwa daruruwan mutane allurar riga-kafin Corona jabu a Yuganda

An gano yadda aka yiwa daruruwan mutane allurar riga-kafin Corona jabu a Yuganda


A kasar Yuganda an yi wa a kalla mutane 800 allurar riga-kafin Corona ta jabu.

An bayyana cewa, an yi allurar riga-kafin ta jabu a asibitoci masu zaman kansu da ke kewayen Kampala Babban Birnin Yuganda.

Jami'in lafiya Warren Namara ya fitar da sanarwa game da batun inda ya ce,

"Daga tsakiyar watan Mayu zuwa karshen Yuni an yi wa a kalla mutane 800 allurar riga-kafin ta jabu a Yuganda.  Watakila an bawa mutane da dama wannan abu."

An kama mutane 2 tare da wani likita game da almundahanar.

Alkaluman Ma'aikatar Lafiya ta Yuganda sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu sama da mutane dubu 79 cutar Corona ta kama a kasar, kuma kusan mutane 900 annobar ta yi ajali. An kuma yi alluran riga-kafi kwaya dubu 843.

Rahotun TRT

0 Response to "An gano yadda aka yiwa daruruwan mutane allurar riga-kafin Corona jabu a Yuganda"

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari