Ko da gaske ne an kai wa Sarkin Kano hari ?


Shàfin labarai na BBC Hausa ta ruwaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta musanta rade-radin da wasu suke yi cewa wani mutum ya kai hari kan tawagar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa wani mutum ne a cikin motarsa ya keta dokar hanya inda ya yi kokarin tafiya duk da yake ba a ba shi hannu ba, lamarin da ya sa ya bangaji wata mota da ke tawagar sarkin.

A cewarsa "yau 25 ga watan bakwai na wannan shekara ta 2021 da misalin karfe 12:45 na rana, akwai rahoto da muka samu cewa hatsari ya hada da tawagar mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero lokacin da yake dawowa zuwa gida ya biyo ta Gadar Lado zuwa sha-tale-talen Dangi, wanda a daidai wannan lokacin an tsayar da motoci... wani direba mai gajen hakuri ya sako motarsa ya bugi tawagarsa ta baya aka samu hatsari."

Ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, an garzaya da direban asibitin Murtala Mohammed aka yi masa magani sannan aka sallame shi.

"Alhamdulillahi, wannan abu bai shafi mai martaba sarki ba. Wanda abin ya same shi ma ya samu sauki. Don haka wannan jita-jita [cewa an kai wa sarki hari] ba gaskiya ba ce. Mai martaba sarki yana cikin koshin lafiya," in ji mai magana da yawun 'yan sandan na Kano.

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN