Kebbi: Duba abin da ya faru a Masallacin kofar gidan Mai Martaba Sarkin Gwandu


An gudanar da addu'oi na musamman domin samun damina mai dumbin yawa da kuma magance matsalolin Yan"ta,adda, fashi da makami, satar mutane da satar shanu a cikin al'umma. 


Abubakar Mu'azu Dakingari, Sakataren watsa labarai na gidan Gwamnatin jihar Kebbi, ya ruwaito cewa, Malaman Addinai sun rokin Allah Madaukakin Sarki da Ya kiyaye kuma Ya shiryar da shugabanni da mabiya a, yayin addu’o’in na musamman da aka gudanar a Masallacin Juma’at da ke bakin Gidan Sarkin Gwandu da ke Nan  Birnin Kebbi a wannan Alhamis.


Limaman da suka jagoranci addu’ar su ne Babban Limamin Gwandu, Malam Ahmadu Rufa’I, Shugaban Makarantun Tsangaya Islamiyya Malam Jabbo da kuma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu  suka yi addu’ar Allah Ya ba da zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.


Muhammadu Lawali, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sarkin Gwandu ne ya jagoranci karatu daga Alkur’ani mai girma a wajen taron wanda Inda Mashawarci na Musamman kan Makamashi Alhaji Yusuf Haruna Rasheed Shima ya Samu halartar Aduu,oin


Babban Limamin Masallacin juna,a na  Walah  Sheikh Ahmad Rufa’I ya gargadi ’yan kasa da su kiyaye takawa, tsoron Allah, da Kuma guje wa ayyukan sabo tare da taimakawa marasa karfi a cikin al’umma.


Sheikh Ahmad Rufa’I ya ce mai martaba Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Ilyasu Bashar ne ya kira taron addu’ar tare da umartar dukkanin Shugabannin Gundumomi da su rinka gudanar da irin wannan zama a kai a kai don neman rahamar Allah da kuma kawo karshen matsalar rashin tsaro a kasa. 

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN