Kungiyar Dattawan Arewa ta yi watsi da kalaman gwamnonin Kudu kan shugabanci


Kungiyar Dattawan Arewa ACF, ta shawarci gwamnonin kudancin Najeriya da su bi tafarkin da ake bi wajen zaben shugabanni daga wurin masu kaɗa ƙuri'a, ba kawai suna zaune a kai musu mulki ba.


Kungiyar ta yi wannan magana ce a matsayin martani kan matsayar da gwamnonin kudancin Najeriyar suka cimma a ranar Litinin, cewa suna son shugaban ƙasar da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudun.


A wata hira da BBC Hausa, kakakin kungiyar Dattawan Arewan Dr Hakeem Baba Ahmed, ya shaida wa BBC cewa kalaman gwamnonin kudun barazana ce kawai wadda ba za ta bai wa 'yan arewa tsoro ba.


Ya ce "Mu a arewa ba sabon abu ba ne mu zaɓi ɗan kudu, mun yi Abiola, mun yi Obasanjo, mun yi Jonathan.


"Kuma ba wanda ya isa ya tilasta mu ya ce dolen-dole ko saboda ban tsoro ko wani abu a ce dole kar wanda ya zabi dan takarar da ba dan kudu ba ko kuma ka da wanda ya jefa ƙuri'a idan ba dan kudu za a jefawa ba.


"Ba wanda ya isa ya yi wannan. Ƴanci muke da shi kamar kowa. Ƴan kudu ɗinnan suna da ƴancin sa ƙuri'a ga wanda suke so. Amma a ce mana mu ba za mu yi ba, wannan kam ba zai yiwuwa ba, in ji kakakin ACF.


Tambaya: A ganinku me ya sa gwamnonin suka yi magana a wannan gaba?

Amsa: Na É—aya dai saboda muna ganin lalacewar Æ´an siyasar Najeriyar ne a yanzu, saboda suna ganin sun rasa yadda za su yi ne su shawo kan jam'iyyunku.


"Don ka ga dukkansu suna cikin manyan jam'iyyu ne na PDP da APC.


"Ku shiga cikin jam'iyyunku ku tabbatar da cewa sun tsayar da Æ´an kudu, kun kasa ne ba za ku iya ba ne, ko kuwa maguÉ—i ne, ko ma dai mene ne dai.'


Tambaya: Amma suna ganin kamar a yi karɓa-karɓa tsakanin kudu da arewa ne

Amsa: "Ba laifi ba ne wannan ma amma ai ba da ƙarfi ake yi ba, ka gane. Karɓa-karɓar nan yarjejeniya ce ƴan siyasa ke yi, amma ba 'yan siyasa ke jefa ƙuri'a ba, jama'a ke yi.


"Idan ya su-ya su ne Æ´an siyasa sai mu bar su. Su Æ´an siyasar ai su suka kawo mana lalacewa. Da PDPn da APCn duka.


"Fadan da suke yi kenan akai nan akai nan sai ka ce idan an je idan ɗan takara ya fito daga kudu sai kuma ka bi dukkan miliyoyin yan arewa ka ce 'to ina yan arewa?' Mu ce ga mu, to yanzu ga ɗan takarar da za ku jefa wa ƙuri'a sai kuma mu yi layi mu ce ba za mu bi ba.


"Mu ba wawaye ba ne, ƴan arewa sun san yancinsu da ƙarfinsu. Wannan abin da ake kuma ba zai ba mu tsoro ba.


"Idan shugabannin kudu za su tashi su yi abin da yan siyasa ke yi su bi mutane su nuna musu fa'idar zaɓen ɗan kudu, to su tashi su yi.


"Amma irin wannan barazanar da ake yi mu ba za ta burge mu ba."


Tambaya: Me ya sa kake kallon hakan a matsayin barazana?

Amsa: "Ai duk wanda y ace maka ko ka yi kaza, ko kuma dole ka yi abu ai barazana ce.


"Kana da Æ´ancin ko ka yi ko kar ka yi fa, sai aka zo aka ce maka ga abin da ake so ka yi, ai barazana ce.


"Ita dimokradiyya ba ta da dole kamar yadda na ce maka.


Tambaya: Me ye ra'ayinku kan yankin da ya kamata shugaban kasa ya fito a 2023?

Amsa: "Mu ba mu da wani ra'ayi illa ra'ayin a bar ƴan Najeriya su zaɓi wanda suka ga ya fi cancanta ya musu mulki.


"Dole wanda zai karɓi mulki daga hannun shugaban ƙasa Buhari sai ya zama ingantacce, karɓaɓɓe wanda kuma ba zai zama shugaban ɓangare ba don ya fito daga can.


"Sai ya zama shugaban ƙasar da zai yi wa kowa adalci. Ka ga ko ba za a zaɓe ka don kawai kai Ibo ne ko Bayerabe ba, a ce kawai don ƙabilarka ko addininka shi ne kawai za mu sa wa ƙuri'a. Saboda me?


"Idan kai kirista ne muna da kirista a Najeriya, ko me kake da shi muna da shi a arewa. Babu wani abu a ciki.


"Abin da muke so shi ne idan ma mulki zai koma kudu, to ya koma da maslaha da magana mai daÉ—i da kuma a nuna mana fa'idar É—an kudu ya zo ya yi mulki."


Matsayar gwamnonin kudu

Ƙungiyar gwamnonin jihohin kudancin Najeriya ta yanke shawara kan matakai daban-daban game da makomar ƙasar a taron da ta gudanar ranar Litinin a birnin Lagos.


Cikin matsayar tasu har da cewa dole shugabancin Najeriya ya kasance na karɓa-karɓa daga yankin arewaci zuwa kudanci.


Kuma suna son shugaban ƙasa da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudancin ƙasar saboda abin da gwamnonin suka kira tabbatar da adalci.


Wannan batu dai shi ne wanda ya fi jan hankalin ƴan arewacin ƙasar.


Sun gudanar da taron ne kwanaki kaɗan bayan jami'an hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, sun kai samame gidan mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawan nan Sunday Igboho, inda suka gano manya-manyan makamai.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN