Kamuwar Allah: Barci ya kwashe barawo bayan ya shiga Masallaci domin ya yi sata da dare a Unguwar Bayan Kara a Birnin kebbi


Allah ya tona asirin wani barawo da ya shiga Masallaci domin ya yi sata amma barci ya kwashe shi a Unguwar Bayan Kara da ke garin Birnin kebbi a jihar Kebbi. Yakubu Ahmed Bk ya ruwaito.

Wanda aka kama, dan shekara 31, mai suna Hamza Usman dan garin Maidahini a karamar hukumar Bunza ya gaya wa jama'a kafin isowar yansanda cewa su uku ne ke wannan harkar sata.

Ya ce biyu sun tsere kuma su ne suke bashi labari da bayanan sirrin gidaje domin ya je ya yi sata, daga bisani sai su raba kudin kayan sata idan an sayar da su.

Bayanin ya ce bayan sun saci wayoyin hannu daga gidajen jama'a, sai Hamza ya bi ta katangar gidan mutane har ya kai Masallaci, ya kuma shiga domin ya saci kayakin amfani a ciki, sai barci ya kwashe shi har Masallata suka iso Masallacin domin yin Sallan Asubah, inda suka tarar da shi kuma asiri ya tonu.

An mika barawon ga jami'an yansanda, kuma sun tafi da shi domin gudanar da bincike. 

Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari