Tap di Jan: dan shekara 23 ya kashe masoyiyarsa mai shekara 46 da yara 4 ya yi lalata da gawarta, duba dalili


An kama wani mutum dan shekara 23 bisa zargin kashe masoyiyarsa mai shekara 46 kuma ya yi wa gawarta fyade.

Adebayo Kingsley, dan asalin garin Ibillo a karamar hukumar Akoko-Edo a jihar Edo, ya kashe Rosemary Ifeoma, wacce mijinta ya mutu ya barta da yara hudu bayan ya kwada mata katako a kai.

Rosemary Ifeoma, wacce aka fi sani da suna Mama Samuel, yar asalin garin Orogun a karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta, ta mutu sakamakon raunin tsananin duka da Adebayo ya yi mata da katako a kai.

Ana zargin cewa Adebayo Kingsley ya yi wa gawarta fyade.

An ce ya kwada wa danta mai shekara 13 katako a kai, yaron ya fadi, sai ya yi zaton cewa yaron ya mutu.

Wannan lamari ya faru ne a Unguwar Darlington Ogbeifun Street, kan hanyar kauyen Ogbekan, a garin Ugbor a karamar hukumar Oredo a jihar  Edo.

Kafin faruwar wannan lamari, Adebayo yana zuwa wajen Rosemary lokaci zuwa lokaci saboda alakar soyayya da ke tsakaninsu kuma hatta makwabta sun San da haka.

Dan mariganyar da Kingsley ya kwada wa katako ya suma, shi ne ya farfado ya gan abin da Adebayo ke yi wa gawar mahaifiyarsa a cikin daki da dare.  

Daga bisani ya je ya gaya wa makwabta kuma suka je da yansanda aka kama Adebayo wanda ya riga ya gudu bayan ya aikata laifin.

Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari