Hotunan yadda aka kama wadanda suka kashe shugaban kasar Haiti da abin da ke faruwa da su yanzu


Mahukunta a kasar Haiti sun kama wasu Yan kasar Amurka guda biyu da Yan kasar Colombia guda 17 bisa zargin kashe shugaban kasar Haiti Joveneil Moise.

Wadanda ake zargi sun yi wa shugan Haiti Juvenel da matar shi Lady Martine ruwan harsashi 12, lamari da ya sa kwayan idon shugaban kasar guda daya ya fito kuma ya mutu, matarshi ta sami munanan raunuka. 

Daga cikin wadanda aka kama har da James Solages, mai shekara 35, da Joseph Vincent, duk yan kasar Amurka amma suna da asalin haihuwa a kasar Haiti. Sauran wadanda aka kama su 15 yan kasar Colombia ne. An kma su ne bayan mumunan harin na ranar Laraba a fadar shugaban kasar da ke tsaunukan Port-au-Prince. 

Shugaban yansandan kasar Haiti Léon Charles, ya ce maharan guda uku ne kawai yansanda suka kashe ba kamar yadda aka labarta a baya ba. Ya ce mutum 8 cikin maharan sun tsere. Ya tabbatar da fuskokin wadanda aka kashe da wadanda suka tsere bayan an gano su ta takardar Fasfo nasu.Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari