Abu 6 da ya kamata ku sani kan muhawarar Malaman Kano da Abduljabbar


A yau Asabar 10 ga watan Yuli ne za a gabatar da muhawara tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malaman addinin Musulunci na jihar Kano a arewa maso yammacin Najeriya.

A ranar Alhamis ne gwamnatin Kanon ta sanya ranar yin muhawarar, kwanaki kadan bayan da shugabannin zauren haÉ—in kan malaman jihar suka zarge ta da "jan kafa", game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa.

Sheikh Abduljabbar ya sha musanta wannan zargi.

A farko gwamnatin ta Kano ta sanya ranar muhawarar kafin daga baya a É—age ranar, kuma a yanzu an samu bambamace-bambamce kan yadda za a gudanar da muhawarar daga tsarin da aka yi da farko.

Ga dai wasu abubuwa shida da wataƙila ba ku sani ba da suka danganci muhawarar:

Malaman da za su fafata

Gwamnatin jihar Kano ba ta bayyana sunayen malaman da za su fafata da Sheikh Abduljbbar Kabara ba a wannan muhawara.

Kwamishinan Al'amuran Addinai na jihar Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ya ce sai a wajen muhawarar ne za a fadi sunayen malaman da za su yi.

Haka kuma a baya, ita ma haÉ—akar malaman ta Kano ta ce ta shaida wa gwamnati malaman da za su wakilce ta, amma ta ce ba za ta bayyana ba sai a zauren muhawarar.

Sai dai sanannen abu ne cewa malamai daga ɓangarorin Ahlussnnah da Izala da Tijjaniya da Kadiriyya ne suke ƙalubalantar Sheikh Abduljabbar.

Wakilin Malaman Ahlussunnah shi ne Sheikh Abdulwahhab Abdullah, sai Shehi-Shehi da ke wakilatar ɓangaren Tijjaniyya, sannan sai Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara da ke wakiltar ɓangaren Ƙadiriyya, wanda yaya ne ga Sheikh Abduljabbar, yayin da Sheikh Abdullahi Pakistan yake wakiltar ɓangaren Izala.

Short presentational grey line

Alƙalai

Ba a faɗi su waye za su yi alƙalancin wannan muhawara ba da kuma waɗanda za su zama masu sa ido.

Su ma sai a wajen taron ne sannan za a sanar kamar yadda Kwamishina Baba Impossible ya ce.

Da wakilin BBC na Kano Khalifa Shehu Dokaji ya tambaye shi dalili, sai ya ce "abin da ya sa ba za a faɗa ba saboda kar a samu uzuri daga wajen wasu da ba za su samu halarta ba a ƙurarren lokaci."

Amma da zarar an kammala taruwa a zauren muhawarar to za a bayyana sunayen alƙalai da masu sa ido kamar yadda ya ƙara da cewa.

Short presentational grey line

Littattafan Sheikh Abduljabbar

Littattafan Sheikh Abduljabbar

ASALIN HOTON,ASHABUL KAHFI

Bayanan hoto,

WaÉ—anda su ne tarin littattafan da Shehin zai je wajen muhawarar da su

Tuni dai gwamnatin jihar Kanon ta amince cewa Sheikh Abduljabbar Kabara na iya tafiya da ɗumbin littattafansa wajen, wadanda yake son yin amfani da su don kafa hujjoji, kamar yadda ya faɗa a wasiƙar da ya aika wa Gwamna Ganduje ta godiya.

Kazalika wani hoto ya yaÉ—u da ke nuna shi da litattafan jibge a gabansa yana nuna alamun ya shirya.

Yawan litattafan da yake shirin zuwa da su sun kai kimanin 300, kuma tuni aka shirya su aka kuma ɗaure su ta yadda za a ɗauke su cikin sauƙi.

Bayan nan malamin ya buƙaci zuwa da mutum hudu da za su ringa taimaka masa wajen ɗaukar litattafan idan buƙatar hakan ta taso, sanna ya roƙi a ba da izinin nuna muhawarar kai tsaye a kafafen yaɗa labarai

Sai dai ga alama gwamnatin Kano ta riga ta yanke hukunci kan yadda tsarin muhawarar zai kasance, ba za a iya sanin ko za ta amsa buƙatun Malam Kabara ko a'a ba har sai an je wajen a gani.

Short presentational grey line

Watsa muhawarar kai tsaye

Ba za a nuna muhawarar kai tsaye a gidajen talabijin ba kuma ba za a watsa kai tsaye a gidajen rediyo ba, sannan ba za a É—auke ta kai tsaye a shafukan sada zumunta ba, kamar yada gwamnati ta ce.

A wancan karon da aka fara sanya ranar muhawarar an bayyana cewa za a watsa ta kai tsaye domin a kalla a kuma saurara.

Amma a wata wasiƙa da Sheikh Abduljabbar ya aike wa Gwamna Ganduje ta amsa gayyatar muhawarar da kuma nuna godiya, ya roƙi gwamnati da ta bari a watsa muhawarar kai tsaye a kafafen labarai.

Sai dai Kwamishinan YaÉ—a Labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya ce an É—auki matakin hana watsa ta kai tsayen ne a wannan karon saboda yanayin tsaro.

"Mun yi hakan ne don tabbatar da tsaron malamai da sauran mahalarta taron," kamar yadda ya shaida wa Khalifa Dokaji.

Gwamnatin ta ce sai an kammala gaba É—aya sannan a yaÉ—a yadda ta kasance.

Short presentational grey line

Ƴan jarida

Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta bar Æ´an jarida da yawa su shiga É—akin taron gudanar da muhawarar ba.

Kwamishinan yaɗa labaran ya ce za su taƙaita yawan ƴan jaridar da za su shiga ciki.

Daga cikin kafafen yaÉ—a labaran da za suka sami izinin shiga har da BBC da Murayar Amurka VOA da kuma wasu tsirarun kafafe na ciki da wajen jihar Kano da ba a bayyana sunayensu ba.

Short presentational grey line

Mahalarta taron

Gwamnati ta ce ba za bar mutane da yawa su shiga wajen muhawarar ba.

A binciken da BBC ta yi ta gano cewa waÉ—anda za a bari É—in Malamai ne da jami'an tsaro da tsirarun Æ´an jarida, da wasu jami'an gwamnati kamar Kwamishinan Yada Labarai da Kwamishina Kula da Harkokin Addinai.

Amma a wasiƙarsa, Sheikh Abduljabbar ya roƙi gwamnati ta bar shi ya je da mutum huɗu, biyu waɗanda za su ɗauki rahoton yadda za ta kasance, sai kuma biyu masu kula da litatttafansa.

Short presentational grey line

Wajen da za a yi

Hukumar Shari'a ta jihar Kano da ke kan titin Abdullahi Bayero ne wajen da za a gudanar da wannan muhawara.

A wancan lokacin da aka saka ranar muhawarar karo na farko a watan Maris, gwamnatin Kano ta ce a Fadar Sarkin Kano za a yi muhawarar.

Sai dai ba ta bayyana dalilin sauya wajen yin muhawarar zuwa Hukumar Shari'a ta Jihar ba.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN