Hotuna da yadda aka kama Pasto da kwarangwam kan dan Adam da wasu kayakin tsafi


Rundunar yansandan jihar Cross River ta kama wani Pasto bisa zargin mallakan kwarangwam kan Dan Adam ba tare da izini ba.

Yansanda sun kama Michael Bassey Dan shekara 45 ne bayan wani mutum ya shigar da koke a kan Michael bisa zargin yin barazana ga rayuwarsa.

Kwamishinan yansandan jihar Mr Sikiru Akande ya ce an kama wanda ake zargin ne a gida mai lamba 56 a Uwanse, kusa da unguwar Asuquo Ekpo a Calabar ta kudu. 

Akande ya ce; 

"An kama Paston ne da kwarangwam kan Dan Adam da aka sassaka daure da hoton wanda ya yi kara a kansa. Tare da wani jar kelle da aka lullube hadi da wasu kayakin tsafi"

Sai da wanda aka kama ya musanta cewa shi bai san komai ba dangane da larin kwarangwam kan Dan Adam. Ya ce shi ba matsafi bane illa mai warkar da jama'a daga sihiri ko sammu da aka yi masu".


Previous Post Next Post

Information


Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/EsSeIwnS18mKkhQwHP3mFx

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari