Gwamna Bagudu ya ziyarci sojin da suke jinya a Asibiti sakamakon raunukan artabu da Yan bindigan a iyakar Kebbi da Zamfara


Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jagoranci Yan Majalisar Dokokin jihar Kebbi a ziyara da ya kai wa sojin da suke jinya a sashe na musamman a Asibitin tunawa da Sir Yahaya a garin Birnin kebbi ranar Alhamis.

Bagudu ya zagaya dakin kulawa na musamman inda babban Likitan Asibitin Sir Yahaya yake kulawa da sojin da kansa, kamar yadda wata majiya ta shaida mana.

Bayan zagayawa tare da yi wa soji masu jinya adduan fatan Allah ya basu sauki. Gwamna Bagudu tare da sauran Yan Majalisar Dokokin na jihar Kebbi da suka mara masa baya a wajen ziyarar tare da shugaban ma'aikatan gidan Gwamnatin jihar Kebbi, sun gudanar da adduar rokon Allah ya jikan sojin da suka rasa rayukansu a wajen aikin samar da zaman lafiya tare da rokon Allah ya ba wadanda suka sami raunuka sauki.

Bagudu ya gaya wa manema labarai bayan ziyarar  a cikin Asibiti cewa ya ziyarci sojin ne domin nuna tausayawa da neman Allah ya jikan wadanda suka mutu kuma ya ba wadanda suka sami raunuka lafiya. Previous Post Next Post

Information

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/J8ryqryDtwR9yvxrOOBlJU

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN