Gwamnati ta rufe asusun kamfanin DSTV da GoTV a Najeriya, duba dalili


Gwamnatin Najeriya ta rufe asusun ajiyar kamfanin nishaÉ—antarwa na Multichoice bisa zarginsa da kauce wa biyan haraji da kuma rufa-rufa ga masu amfani da manhajarsa.

Hukumar tattara haraji ta ƙasar, Federal Inland Revenue Service (FIRS), na neman kusan da dala biliyan huɗu da rabi daga sashen kamfanin na Najeriya wanda mallakar Afirka Ta Kudu ne.

Kazalika, hukumar ta zargi kamfanin da ƙin amsa takardun bayanan da ta nema daga wajensa.

Duk da cewa kashi 30 cikin 100 na ribar da kamfanin ke samu daga Najeriya ne amma Multichoice ya ƙi ya bai wa FIRS damar duba rumbun ajiyar bayanansa domin yin lissafi, a cewar shugaban hukumar Muhammed Nami.

Sai dai kamfanin ya mayar da martani da cewa yana "bin dokokin biyan haraji na Najeriya", sannan kuma yana tattauna wa da FIRS "domin shawo kan matsalar cikin ruwan sanyi"

FIRS ta umarci bankuna da su taimaka mata domin ƙwato dala biliyan 4.4 - kwatankwacin naira tiriliyan 1.6 - wanda ta ce haraji ne da gwamnati ke bin kamfanin bashi.

Multichoice ne ya mallaki kamfanonin DSTV da GoTV, waÉ—anda su ne kamfanonin samar da tashoshin talabiji na tauraron É—an Adam mafiya girma a Najeriya, kuma da ma sun sha kai ruwa rana da gwamnatin a kwanan nan.

A watan Yunin 2020 'yan majalisar Najeriya suka ƙaddamar da wani bincike game da ayyukan kamfanin a ƙasar kan yawan cazar kuɗi da kuma ƙin aiwatar da tsarin biyan kuɗi daidai da abin da mutum ya kalla wato pay-per-view a DSTV da GoTV.

Ba wannan ne karon farko da kamfanin Afirka ta Kudu ke shiga matsala ba a Najeriya. Gwamnati ta ci tarar MTN dala biliyan 5.2 ssaboda ya gaza toshe layukan salula miliyan 5.2 marasa rajista. Kodayake an rage tarar zuwa biliyan 3.4 daga baya.

Wakilin tattalin arziki na BBC a Legas ya ce wannna wani lokaci ne na musamman da Najeriya ke ƙoƙarin haɓaka hanyoyin samun kuɗin shigarta musamman daga kamfanonin ƙasar waje.

Ana sa ran gwamnati za ta ɗauki ƙarin matakai a kan wasu kamfanonin da ake zargi da kauce wa biyan haraji.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN