Duba abin da aka yi wa wasu mutane da ake zargin suna aikata Luwadi a jihar Kano


Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da aikata luwadi a unguwar Sheka Barde a karamar hukumar Kumbotso.

Shugaban hukumar Harun ibn-Sina ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, BBC ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta tattaro, a cewar sanarwar wasu mazauna yankin ne suka shigar da kara kan wannan batu.

An kwamushe wasu da ake zargi da aikata luwadi a jihar Kano

Harun ya ce:

"Duka wadanda ake zargin sun haura shekara 20, mun kuma kama su ne a ranar 11 ga watan Yuli a wani samame na musamman."

Shugaban hukumar ya nuna rashin jin dadi kan wadannan matasa da aka kama.

Ibn-Sina ya yi wa 'yan yankin godiya da kuma masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da suka bayar da hadin kai wajen kama wadannan mutane.

Ya ce za a mika wadannan mutane da aka kama zuwa kotu.

‘Yan luwadi sunyi fada bayan kamuwa da cutar kanjamau a jihar Legas

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, an samu hatsaniya, a Egbe, Ikotun dake jihar Legas, inda wasu masu luwadi sukayi fada da junansu bayan kmauwa da cutar kanjamau.

Ezeugo daya daga cikin masu luwadin shine ya sanyawa masoyin nasa cutar, bayan ya kawo wani zaiyi luwadin dashi sai na farkon ya tayarda hayaniya a cikin gidan da misalin karfe 3 na dare a ranar Talata.

Mutanen Unguwa dole tasa suka kirawo jami’an ‘Yan Sanda na Ikotun, inda suka kama wadanda ake zargin. Inda Ezeugo ya masawa hukumar ‘Yan Sanda cewa ya kai shekara biyar yana luwadi.

Source: Legit News

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN