Da gaske ƙarfe na maƙalewa a hannun waɗanda aka yi wa riga-kafin cutar?


Wani batu da ke jan hankalin mutane a shafukan sada zumunta musamman a kwanan nan shi ne yadda ake yaɗa bidiyon cewa wasu nau'ukan ƙarafa kamar makulli na maƙalewa a jikin duk wanda aka yi wa allurar riga-kafin cutar korona.

Mutane sun riƙa sanya makulli a hannunsu yana maƙalewa ba tare da ya faɗi ba domin tabbatar da cewa riga-kafin cutar ta korona yana da haɗari ga jiki, da kuma lafiyar duk wanda aka yi wa.

To sai dai mutane da dama da ke bayyana ra'ayoyinsu sun riƙa nuna shakku a kan sahihancin abin da mutanen da ake nunawa a bidiyon ke faɗi.

Wasu ma na zargin cewa su na sanya mayen ƙarfe ne a hammatarsu domin tabbatar da abun da suke faɗa.

Ga wani bidiyo da aka yaɗa.

Kauce wa Instagram, 1

Karshen labarin da aka sa a Instagram, 1

Wannan layi ne

''Labarin ƙanzon kurege ne''

A cewar Farfesa Abdussalam Nasidi, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya ko kaɗan wannan abin da mutanen da ake nunawa a wadannan bidiyon ba gaskiya ba ne.

Ya ce labari ne na ƙanzagon kurege da suke yaɗawa da manufar yaki da ƙokarin mahukunta na son kawar da annobar korona a Najeriya.

''Ni na ga wannan bidiyo da ake magana a kansa, kuma abin da nake son gaya wa jama'a shi ne dukkanin riga-kafin cutar korona da ake amfani da shi a duniya babu wanda ke dauke da wani sinadari na ƙarfe ko wani abu mai kama da haka.

"Don haka babu ma batun yin tunanin cewa shi aka sanya maka a jikinka, ka daura wani ƙarfe a jikin zai maƙale'', a cewar Farfesan.

Ya ƙara da cewa ita kanta ana zurkuɗa ta ne can cikin jiki, wato ratsa tsoka take yi ta shiga ba wai a kan fata ake yin ta ba, ballantana mutane su yi tunanin cewa wannan ne dalilin da kan sa ƙarfen ya kama jiki.

''Wani abu da muka lura da shi, shi ne su waɗannan masu yada labaran suna shafa garin mayen ƙarfe ne kafin su sa abun da suke son sa wa a hannunsu domin su nuna suna da gaskiya.

"Wasu kuma suna sanya mayen ƙarfen ne a hammatarsu'', in ji shi.

Yadda wani mutum ya warware ƙaryar

Kauce wa Facebook, 1

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 1

Wannan layi ne

Ba wannan ne farau ba

Prof Abdulsalam Nasidi
Getty
Masu yada labaran ƙaryar na shafa garin mayen ƙarfe ne kafin su sa abin da suke son sa wa a hannunsu don su nuna suna da gaskiya. Wasu kuma suna sa mayen ƙarfen ne a hammatarsu."
Farfesa Abdulsalam Nasidi
Ƙwararre a harkar lafiya kuma tsohon shugaban NCDC

Ba dai wannan ne karon farko da ake yaɗa labaran ƙanzon kurege a kan cutar korona ko ma riga-kafin cutar a shafukan sada zumunta a kasashe da dama na duniya ciki har da Najeriya ba.

Farfesa Abdussalam Nasidi ya bayyana wa BBC cewa an jima ana baza irin waɗannan labarai da nufin yin zagon ƙasa da kokarin ganin an gamsar da kowanne dan kasa ya karbi riga-kafin korona.

''An sha cewa shi wannan riga-kafi yana janyo daskarewar jini, ka ga wannan labari ba gaskiya ba ne. An sha cewa an kawo riga-kafin Afrika ne ma domin wai a rage yawan al'ummar wannan kasa, ka ga shi ma wannan ba gaskiya ne ba, irin wadannan ƙarairayi na nan da yawa'' in ji Farfesa Nasidi.

Gwamnatin Najeriya ta sha jan hankalin 'yan ƙasar game da yaɗa jita-jita a kan riga-kafin, ta na cewa ba za ta lamunci kawo ma ta cikas a shirinta na yi wa jama'a riga-kafi ba.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN