Yanzu yanzu: Yan bindigan daji sun sace basaraken arewa mai daraja ta 2 tare da wasu mata da yaransa su 12


Yan bindigan daji sun kutsa cikin gidan Sarkin Kajuru Alhaji Hassan Adamu suka dauke shi a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna. Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika Yan bindigan sun yi awon gaba da mutum 12 cikin iyalinsa da suka hada da mata da yara.

Wani jikan basaraken wanda kuma shi ne ke rike da mukamin Dan Kajuru, Sa'idu Musa ya tabbatar wa Wakilin Daily trust da faruwar Lamarin .

Ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 12:30 na dare.

Cikakken labari anjima.......

 • 0/Post a Comment/Comments

  Rubuta ra ayin ka

  Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari