Cikakken rahotun yadda yan bindiga suka sace Basarake a Arewacin Najeriya da iyalansa


Rahotanni daga jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a masarautar Kajuru inda suka sace Sarkinta Alhaji Alhassan Adamu da wasu iyalansa.

Ganau sun tabbatar wa BBC Hausa cewa an sace sarkin ne da iyalansa 13 a harin da 'yan bindigar suka kai da tsakar daren jiya.

Wani mutum da ba ya so mu ambaci sunansa ya ce an sace sarkin, mai shekara 85 tare da mata uku, jikokinsa biyu, ma'aikatansa uku da kuma karin mutum biyar.

Na cire ɗana daga makarantar gwamnati saboda 'yan fashi na ƙoƙarin sace shi - El-Rufai

Manyan dazukan da Æ´an ta'adda ke samun mafaka a arewacin Najeriya

Kawo yanzu hukumomi ba su ce komai a kan lamarin ba.

Sai dai bayanai sun nuna cewa sarkin ya gudanar da taro ranar Juma'a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa.

Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako guda da sace daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist fiye da 100 da ke karamar hukumar Chukun a jihar ta Kaduna.

Kazalika harin na zuwa ne mako guda bayan sace wasu mutane, ciki har da jarirai, a asibitin masu larurar kuturta da tashin-fuka da ke Zaria.

Jihar Kaduna na fama da hare-haren 'yan bindiga inda wani rahoto da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar ta fitar a watan Afrilu ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar.

Gwamnatin jihar ta Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Nasir Elrufai, ta sha jaddada cewa ba za ta yi sulhu da 'yan bindigar da ke garkuwa da mutane ba, tana mai cewa babban burinta shi ne ta kawar da su.

Rahotun BBC

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN