An yi wa wani tsoho dan shekara 63 a Duniya bulala 10 a bainar jama'a kuma aka ci shi tarar kudi shs100,000 saboda yana neman diyar matarshi domin ya yi lalata da ita a kauyen Akero da ke gundumar Bukedea a kasar Uganda.
Wani Dattijo da ake martabawa na kauyen mai suna Martine Okwii, ya ce wanda aka ladabtar mai suna Moses Oluka, ya sha aikata lalata da diyar matarshi.
Shafin labarai na isyaku.com ya samo cewa diyarv matarshi mai suna Alupo Jessica tare da mijinta Akol Samuel, suka kai karar mijin mahaifiyarta saboda yadda yake damunta da harkar jima'i.
Mijin Jessica ya ce mijin nahaifiyar matarshi ya sha takura wa matarshi da harkar jima'i ba tare da son ta ba.
Sakamakon haka Dattijan kauyen suka kafa kwamiti da ya bincika lamarin kuma aka zartar da hukuncin bulala 10 a kan tsohon kuma a bainar jama'a, daga bisani aka ci shi tara biyan akuya daya da kudin kasar Uganda shs100,000.
An zartar masa wannan hukunci ne ranar Talata 27 ga wata Yuli.