Yadda Kaka da katti 10 suka yi wa jikanya duka da sanduna har ta mutu saboda ta saka wandon Jeans


Yan uwa da iyalin wata yarinya mai suna Neha Paswan, mai shekara 17, sun yi mata dukan ajali a Uttar Pradesh, na kasar  India saboda ta sa wandon Jeans.

Mahaifiyar Neha mai suna Shakuntala Devi Paswan ta gaya wa sashen Hindi na gidan rediyon BBC cewa wasu mutane daga cikin iyalinsu ciki har da Kakan Neha dauke da sanduna suka yi mata duka har ta mutu.

Shakuntala ta ce bayan Neha ta yi azumi tsawon rana, ta sauko daga matakalin gida sanye da wandon Jeans. Amma sai Kakanta ya nuna rashin jin dadi cewa ta saka wandon Jeans, kuma lamarin ya haifar da matsala domin Neha ta gaya wa Kakanta cewa an yi wandon Jeans ne domin a saka shi.

Barkewar rigimar ke da wuya sai maza 10 masu tsatsaurar ra'ayi suka zo da sanduna suka dinga jibgan Neha har ta mutu, kuma suka yi kokarin su boye lamarin bayan ganin cewa Neha ta mutu.

 

Previous Post Next Post